Motocin dakon mai na Dangote masu amfani da iskar gas ta CNG sun fara lodin mai a matatar don yin dakonsa kyauta a faɗin ƙasar.
Wakilan kafafen yaɗa labarai da dama na Nijeriya da suka halarci ƙaddamarwar a ranar Litinin sun ce tuni rukunin farko na motocin suka hau layi don yin lodin man.
Tun a watan Agustan da ya gabata ne Matatar ta ce ta karɓi rukunin farko na manyan motocinta na CNG guda 4000, waɗanda za su dinga dako a faɗin ƙasar, wanda tun da fari aka so farawa a ranar 15 ga Agustan.
A wata ziyarar ban girma da Cibiyar AfricaRice ta kai a ofishinsa da ke Legas a ranar Lahadi, Aliko Dangote ya sake nanata cewa matakin da ta dauka na daukar matakin raba mai kai-tsaye shi ne rage dogaro da kamfanonin da ke dakon mai a Nijeriya.
A cewarsa, matakin ba wai kawai wani tsari ne na zaɓi ba, amma wani lamari ne mai mahimmanci ga ƙasa baki daya.
Kai ruwa rana
An yi ta kai ruwa rana a kan wannan lamari tun bayan sanarwar da Dangote ya yi na fara wannan jigila kyauta.
Tun da fari a farkon watan Agusta, ƙungiyar masu sayar da mai da gas a Nijeriya (NOGASA) ta yi gargaɗin cewa idan har Matatar Mai ta Dangote ta ci gaba da shirinta na fara dakon fetur da gas a faɗin ƙasar da isar da su kai-tsaye ga masu sayarwa maimakon bi ta hannun masu dakon man, to ƙasar za ta fuskanci tarnaƙi wajen samar da mai da ma fama da rashin mai na tsawon lokaci tare da durƙushewar tsarin dakon mai da ƙasar ke bi a halin yanzu.
Masu sayar da man sun nemi Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya sa baki a lamarin, suna cewa dakon mai a faɗin Nijeriya a ƙarƙashin Matatar Dangote ba zai ɗore ba.
Ita ma Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan da ke dakon man fetur da Gas a Nijeriya (NUPENG) ta yi barazanar shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani a farkon watan Satumba tare da hana mambobinta dakon mai a faɗin ƙasar duk don shirin Matatar Man Dangote na dinga kai mai ga masu sayarwa da kai-tsaye.
Sannan a makon da ya gabata ma Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (DAPPMAN) ta zargi matatar da “bayar da farashi mai rahusa ga masu saye a kasashen waje yayin da ta yi la’akari da karin farashin ga ‘yan kasuwa na cikin gida.”