Batun auren Mai Wushirya da 'Yar Guda ya ja hankali a shafukan sada zumunta a Nijeriya
Batun auren Mai Wushirya da 'Yar Guda ya ja hankali a shafukan sada zumunta a Nijeriya
Abba El-Mustapha wanda shi ne ya karbi belinsu ya ce ya miƙa su ga hukumar Hizbah don a fara shirye-shiryen ɗaura musu aure bayan an kammala gwaje-gwajen lafiyarsu.
14 awanni baya

Mutane na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu bayan wata kotun majistare a Jihar Kano ta umarci a ɗaura auren fitaccen ɗan TikTok ɗin nan Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya da wata mata da yake yin bidiyo da ita, wato Basira ’Yar Guda a cikin kwana 60.

An dauki wannan matakin ne bayan Mai Wushirya da ’Yar Guda sun yarda suna son junansu kuma suna son su yi aure a tsakaninsu yayin da ake musu shari’a a gaban kotu, kamar yadda Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha ya bayyana wa manema labarai.

Abba El-Mustapha wanda shi ne ya karbi belinsu ya ce ya miƙa su ga hukumar Hizbah don a fara shirye-shiryen ɗaura musu aure bayan an kammala gwaje-gwajen lafiyarsu.

Shugaban Hukumar Hizbah Sheikh Aminu Daurawa ya shaida wa manema labarai cewa sun riga sun fara shirye-shiryen auren ’yan Tiktok ɗin kuma ya ƙara jadddada cewa za a yi auren ne saboda Mai Wushirya da ’Yar Guda sun nuna sha’awar yin hakan.

Babban malamin addinin Musuluncin ya ce yanzu za a yi wa ’yan TikTok ɗin gwaje-gwajen lafiya kafin a ɗaura musu aure, kamar yadda dokokin Jihar Kano suka buƙata.

A farkon watan nan ne kotun ta bayar da umarnin a tura Ashiru gidan gyaran hali na tsawon mako biyu saboda wallafa bidiyon batsa a dandalin sada zumunta.

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano ce ta kama Mai Wushirya kimanin makonni uku da suka gabata bayan ya wallafa wasu hotunansa ba riga tare da ’Yar Guda.

Tun kafin kamun, Mai Wushirya ya kwashe lokaci yana wallafa hotunansa tare da ’Yar Guda a shafukan sada zumunta.

Sai dai jim kaɗan bayan umarnin da kotu ta bayar na ɗaura auren Mai Wushirya da ’Yar Guda mutane suka riƙa bayyana mabambantan ra’ayoyi musamman a kafafen sada zumunta dangane da batun.

Yayin da wasu suke farin ciki da matakin har ma wasu suke cewa za su bayar da gudunmuwar sadaki da sauransu, wasu kuwa suna nuna rashin jin daɗinsu ne da matakin kuma suna cewa abin ba zai haifar da alheri ba zuwa nan gaba.

Masu sharhi da dama sun musanta ra’ayin Abba El-Mustapha na cewa auren zai zama na dindindin, a ganinsu babu wani aure a duniya da za a sha masa alwashin zai zama na mutu-ka-raba, don komai zai iya faruwa bayan auren.

Sai kuma wasu masu sharhi da suke ganin da ma can Ashiru yana yin duk abubuwan da yake yi ne don neman suna da son ya yi trending.

Saboda haka suna ganin idan gwamnatin Kano ta yi masa aure da ’Yar Guda a halin yanzu kamar an taimaka wa Mai Wushirya ne wajen cim ma wancan babban burinsa na ci gaba da yin trending.

A ganinsu, hakan zai buɗe ƙofar wasu ma a nan gaba su ma su yi amfani da irin wannan salo da Ashiru ya yi amfani da shi wajen biyan buƙatarsa ta neman suna ta ko wane hali.

A hannu guda kuma akwai masu ganin matakin ɗaura wannan aure ya dace, saboda a cewarsu, Mai Wushirya yana amfani da ‘Yar Guda ne wajen aibata tsarin halittarta don samun kuɗaɗen content creation.

Suna ganin kuma yana hakan ne don ganin ba ta da gata da mai tsaya mata don kare martabarta wajen yin abubuwan da yake yi da ita.

A ganin masu irin wannan ra’ayi, hukumar Hisbah ta zama gatan ‘Yar Guda wajen kare ƙimarta da mutuntakarta.

Sharuɗɗa

Sai dai kamar yadda Shugaban Hisbah, Sheikh Daurawa ya yi jawabi, ya ce tuni ‘Yar Guda ta saka wasu sharuɗɗa da ta ce idan Mai Wushirya bai cika su ba to ba za ta aure shi ba.

Malamin ya ce ‘Yar Guda ta ce lallai sai Mai Wushirya yana da gidan kansa, ba na haya ba, ba kuma na gado ba, sannan ne za ta yarda da auren.Don haka Malam ya ce za su duba su ga sharaɗin ya dace da shari’a ko bai dace ba.

Amma a hannu guda, Daurawa ya ce shi Mai Wushirya bai saka wani sharaɗi ba tukunna.

Sai bayan an kammala waɗannan matakai ne sannan za a saka ranar aure har ma da shirya walima.