Nairobi Birdman: Matashin da ke abota da tsuntsaye a Kenya
Ya shafe shekaru 13 a kan tituna, yana samun mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi ba tare da wani ya kula da shi ba.
Nairobi Birdman: Matashin da ke abota da tsuntsaye a Kenya
Wani matashi a Kenya wanda ya shafe shekara 13 yana rayuwa ba tare da muhalli ba, ya yi fice a kan titunan Nairobi babban birnin ƙasar sakamakon yadda ake abota da tsuntsaye
29 Yuli 2025

Tsuntsaye uku sun cikin kwanciyar hankali sun zauna a jikin wani mutum – biyu a kafadunsa, ɗaya a kansa – inda yake yawo da su a kan titunan Nairobi.

Yayin da mutane ke juya kansu suna ganin shi tare da waɗannan tsuntsaye, ba tare da ɗaukar lokacin ba suke fahimtar irin dangantaka mai ƙarfi da ke a tsakaninsu.

Ga Rodgers Oloo Magudha, wanda ya shafe shekara 13 yana rayuwa ba tare da muhalli ba, inda haɗuwarsa da abokansa masu fiffike ta sa ya yi fice a cikin birni.

"Mutane suna kirana da 'Nairobi Birdman'," wato mai tsuntsaye na Nairobi in ji Rodgers a tattaunawarsa da TRT Afrika. "Idan ka kalle ni, zaka gane wane ne ni."

Daga titi zuwa mai kula da dabbobi

An haifi Rodgers a Nakuru, kimanin kilomita 170 daga babban birnin Kenya, Nairobi, kuma mahaifiyarsa ce kaɗai ta raini shi. Rayuwarsa ta canza gaba ɗaya lokacin da mahaifiyarsa ta rasu.

Ya shafe shekaru 13 a kan tituna, yana samun mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi ba tare da wani ya kula da shi ba.

Lokutan kadaici sau da yawa suna haifar da abubuwan ban mamaki na samun abota. Wata rana, wani ƙaramin tsuntsu mai rashin lafiya ya ja hankalin Rodgers, wanda ya zama wani sabon babi a rayuwarsa mai cike da ƙalubale.

Cike da tausayi, ya ɗauki tsuntsun, yana kula da shi har ya warke ta hanyar ba shi abinci, soyayya da kulawa. Wannan sabon abokin nasa mai fiffike bai taɓa barin gefensa ba tun daga lokacin.

Rodgers yana kira tsuntsun da suna Johnson, wanda suna ne yanzu da ya yi fice a kan titin Nairobi.

Amma labarin bai tsaya ga marar gida da ya samu abota da tsuntsu ba. Johnson ya ba Rodgers ma'ana a rayuwarsa da ya rasa.

"Mun haɓaka wata alaƙa ta musamman. Ya zama abokina da muke tare kullum a kan titi. Johnson yana iya bin umarnina; har ma yana hawa kafadata idan na ce masa ya yi haka," in ji Rodgers.

Sauran tsuntsaye biyu da ke tashi yayin da suke zaune a kafadunsa su ma suna da labaransu.

"Wannan a kafadata ta hagu ana kiranta Joan, ɗayan kuma Jaime. Dukansu mata ne. Na sanya wa Joan suna ne saboda tsohuwar budurwata Joannitta, domin in riƙa tunawa da ita," in ji Rodgers ga TRT Afrika.

Shan wahala a tare

Rayuwa a kan titi ta kasance mai wahala. Kulawa da tsuntsaye uku ya kasance ƙarin wahala ga a "Nairobi Birdman".

"Wadannan tsuntsaye na cikin dangin black kite. Yawanci ina ba su nama ɗanye, amma idan ba zan iya siya ba, muna amfani da abin da muke da shi domin mu tsira tare," in ji shi.

Haka kuma dole Rodgers yana fama da masu yi masa wani kallo na rashin yarda inda suke kallon dangantakarsa da wannan tsuntsaye kamar shiri ne.

"Na taɓa ji mutane suna zargina da sihiri. Amma Allah Mai Girma ya ba mu duniya don mu yi rayuwa da waɗannan halittu, don haka babu wanda zai iya yanke mini hukunci. Ina kula sosai da waɗannan tsuntsaye, kuma su ma suna ƙaunata."

Sha'awar Rodgers da ƙoƙarinsa na zama fiye da abin sha'awa ya zarce halin da yake ciki a yanzu.

Yana fatan gina gidan marayu inda zai iya kula da ƙarin tsuntsaye kuma ya ƙirƙiri cibiyar da mutane za su iya ziyarta don ganin nau'ikan tsuntsaye daban-daban.

Haka kuma yana mafarkin kafa cibiyar ceto ga abin da yake kira "al'ummar titi."

"Tituna gida ne ga mutane da iyalansu suka manta da su ko suka bari. Ina son yin wani abu da zai ba su ƙarfi, ciki har da ƙwarewar rayuwa," in ji Rodgers.

Yayin da burinsa ke ci gaba da ƙaruwa, yana cikin tunani sosai yayin da yake magana game da abokansa tsuntsaye.

"Ko da yaushe zan je, waɗannan tsuntsaye za su kasance tare da ni. Tsuntsaye suna taka muhimmiyar rawa a tsarin halittu, musamman a cikin yanayin sauyin yanayi da tasirinsa. Dole ne mu kula da su ta kowace hanya," in ji Rodgers.

Don haka, shin ya taɓa yin tunani game da yanayin ban mamaki na alaƙarsa da tsuntsaye? "Ina tsammanin a wata rayuwa ta daban, zan kasance tsuntsu," kamar yadda ya bayyana.

Rumbun Labarai
Yadda ɗaliban Nijeriya suka samu zantawa da ‘yar-sama-jannati da ke Tashar ISS a sararin samaniya
Yadda dafa abinci na haɗin gwiwa a Somaliya ke ciyar da ɗaruruwan Falasɗinawa a Gaza
Hilda Baci: Fitacciyar mai girki ta Nijeriya ta dafa buhu 200 na shinkafa a yunƙurin kafa tarihi
Sabon nazarin WHO da ke shawartar a daina dukan yara da nufin gyaran tarbiyyarsu
Yadda ƙasaitaccen bikin 'yar hamshakin attajirin Nijeriya Femi Otedola, Temi ya ɗau hankali
Hotunan yadda dubban Musulmai a ƙasashen duniya suka yi murnar Maulidin Annabi
Ranar Hausa ta Duniya ta 2025 ta ƙayatar da gagarumin biki a Daura
Manufar bai ɗaya ta tsare harshe ta hade kawunan al’ummar Songhay-Zarma-Dendi
Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi bayan ya gabatar da shirye-shiryen rediyo mafi tsawo a tarihi
Amaren Gaza: Matan da yaƙin Isra’ila ya mayar zawarawa rabi da rabi
Yadda bikin Rahama Sadau ya zo da mamaki amma ya samu yabo
Hotunan yadda ake tashin talakawa masu kwana a titi a birnin Washington na Amurka
Hijirar tsuntsaye: Afrika na tattaro kan duniya wajen ceto muhimman fadamu don biliyoyin tsuntsaye
Tsutsar Mopane: Daddaɗan abincin Namibia da ake ci tsawon zamanai
Maryam Bukar Alhanislam: 'Yar Nijeriyar da ta zama jakadiyar zaman lafiyar MDD ta farko a duniya
Dalilan da suka sa ake buƙatar mutane su samu abokai na zahiri a yayin da intanet ke jawo kaɗaitaka
Yadda birai suka addabi wani gari a Afirka ta Kudu da "sata da ƙwace"
Abin da ya sa Kabul zai iya zama babban birni na farko da zai fuskanci matsalar rashin ruwa a duniya
Bikin Wasannin Al’adu Karo na 7 ya farfado da hadin kan al’adu, iyalai da ma duniya
Waiwaye kan tarihin Aikin Hajjin Annabta da yadda ake gudanar da shi