| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Nijeriya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon bashin $1.25bn: rahoto
Lamarin na zuwa ne kwanaki bayan Akanta Janar na Nijeriya, Dakta Shamseldeen Ogunjimi, ya yi gargaɗin cewa Nijeriya za ta iya yin watsi da shirin karɓar bashin Bankin Duniya idan jinkiri kan amincewa da shi ya zarce watanni shida.
Nijeriya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon bashin $1.25bn: rahoto
Wannan na zuwa kwanaki bayan babban akantan Nijeriya ya yi gargadin cewa ƙasar za ta iya ƙin rancen bankin duniyar idan jinkiri ya zarce wata 6 / Reuters

A yanzu haka gwamnatin tarayyar Nijeriya tana tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon lamuni na dala biliyan 1.25, in ji wani labari da gidan talbijin mai zaman kansa na Channels Television na Nijeriya ya ruwaito.

Rahoton ya ambato wata takarda da gidan talbijin ɗin na Channels ya gani mai taken ‘Matakan Nijeriya na zuba jari da gaggauta [samar da] ayyukan yi’, wadda ta bayyana cewa rancen da ake magana zai ɗauki nauyin gyara tattalin arzikin da ake yi da samar da ayyukan yi da iya gogayya.

Takardar ta ce tattaunawar na mataki mai muhimmanci inda ake sa ran gabatar da batun domin amincewa da shi a ranar 26 ga watan Yuni na shekarar 2026. Bashin ya tsallake matakai na farko na bayani da gwaji a gaban hukumomin Babban Bankin.

Idan aka amince da shi, zai kasance rance na biyu mafi yawa da bankin zai bai wa ƙasar tun bayan da ya amince da bashin $1.5b a watan Yunin shekarar 2024.

An bayyana mai karɓar bashin a matsayin Tarayyar Nijeriya yayin da ma’aikatar kuɗin Nijeriya ce za ta yi aiki a matsayin hukuma mai zartarwa.

Bashin da Nijeriya ta karɓa daga ƙasashen ƙetare daga ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2025 ya kai dala biliyan 51.86, yayin da a halin yanzu jumullar bashin da ke kan ƙasar ya kai dala biliyan 110.97.

A halin yanzu bashin yana matakin yanke hukunci ne a Bankin Duniya, wani mataki da masu gudanarwa na masu ba da bashin ke bibiyar tsarin bashin domin yanke hukunci kan ko ya kamata a miƙa aikin ga majalisar daraktoci na zartawar Bankin Duniyar domin amincewa ko kuma a’a.

Wannan matakin na zuwa ne bayan an kammala nazari da kuma yarjejeniya sannan a cim ma matsaya kan muhimman matakai na manufa da ƙa’idojin biya da kuma jajircewa kan gyara tsakanin mai karɓar bashin da tawagar Bankin Duniya.

A matakan rancen bankin duniyar zaman yanke shawara shi ne zama na ƙarshe a amincewa daga cikin bankin, kuma daga nan ne za a shirya tsarin domin amincewa ta ƙarshe ta hukumar gudanarwa.

Takardar ta bankin duniya ta bayyana cewa, “nazarin ya bai wa tawagar damar kimanta da kuma yajejeniya,” abin da ke nufin cewa shirin ya tsallake bincike na cikin gida kuma yana kan hanayarsa ta amincewa ta ƙarshe.

Bankin duniya ya ce bashin an tsara shi ne “domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin na faɗaɗa damar samun hidima na lantarki da intanet da kuɗi kuma da ƙarfafa gasa ta gyaran haraji da cinikayya da noma.”

Bankin duniya ya amince da bashin kimanin dala biliyan $9.35 ga Nijeriya daga watan Yunin shekarar 2023 zuwa watan Mayun shekarar 2026.

Rumbun Labarai
’Yanbindiga sun kashe mutum 17 a Jihar Zamfara a Nijeriya
Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 25 a Borno, sun ƙwato makamai
Nijeriya ta rage dogaro da kuɗaɗen shiga daga ɓangaren man fetur sosai – Tinubu
Shugaba Tinubu da Christopher Musa sun sake nazari kan tsarin tsaro da kariya na Nijeriya
Nijeriya ta ayyana zaman makokin kwana uku kan sojojin da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Ondo
Jirgin sama na sojin Nijeriya ya yi hatsari a Jihar Ondo
Malamai 300,000 daga 700,000 ne ba su da ƙwarewa a Nijeriya – Majalisar Rajistar Malamai
An kashe mutane 28 duk da dokar hana fita a jihar Filato a Nijeriya - Rahotanni
Gwamnonin Arewa maso-gabashin Nijeria sun yi shelar kafa kamfanin jiragen sama na yanki
Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa, in ji Kashim Shettima
Yawan iskar gas ɗin da Nijeriya ke samarwa a cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2
Mutfwang ya gana da Tinubu, ya ce an fara gurfanar da masu kai hare-hare a Filato
'Yansandan Nijeriya sun ceto mutane 10 daga cikin 'yan NYSC da aka yi garkuwa da su a jihar Imo
Nijeriya: Mutane uku sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin kuɗi a Jihar Neja
Ranar 'Yancin Kai a Nijeriya: Sauye-sauyen da muke yi za su haifar da sakamako mai kyau - Tinubu
Dubban fasinjojin Kano da suka bi Saudi Airline sun koka cewa kayansu sun maƙale a Saudiyya
Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaddamar da motocin yaƙi masu sulke da bataliyar soji uku a jihar Kebbi
'Yansandan Nijeriya sun gano ƙoƙon kawuna 28 a wani daji a Jihar Abia
Kotun Nijeriya ta umarci NMDPRA ta bai wa A.A Rano, AYM Shafa da Matrix lasisin shigo da fetur
An sace fiye da mutum 80 a cikin mako biyu a arewacin Nijeriya