Dakarun rundunar Operation Enduring Peace sun kashe wasu gawurtattun masu garkuwa da mutane kana suka kuɓutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a jihohin Kaduna da Filato.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Litinin ta ce dakarun rundunar sun kai samame mafakar masu garkuwa da mutane a ƙauyukan Dangoma da Godogodo da ke ƙaramar hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna sakamakon yadda ake ta garkuwa da mutane a yankin.
“A lokacin arangamar, an kashe masu garkuwa da mutane uku. Sauran ‘yan bindigar sun tsere ɗauke da raunin bindiga. Ana ƙoƙarin kama waɗanda ake zargin da suka tsere,” in ji sanarwar da Manjo Samson Nantip, jami’in watsa labaran rundunar, ya sanya wa hannu.
Kazalika ranar 12 ga watan Disamba dakaru sun yi nasarar kai samame a maɓiyar wani ƙasurgumin ɓarawo da ya yi ƙaurin suna a garkuwa da mutane a ƙananan hukumomin Bassa da Jos North na Jihar Filato, in ji sanarwar.
“An kama wanda ake zargin ne a kan hanyar Jebbu zuwa Gada Biu a ƙaramar hukumar Bassa. Yana ganin jami’an tsaro kawai, sai mai aikata laifukan ya buɗe musu wuta, amma nan-take dakarun suka harbe shi. Ababen da aka ƙwace daga gare shi sun haɗa da wata ƙaramar bindiga da harsasai tara da wuƙa ɗaya da waya ɗaya da kuɗi mai yawa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ranar 13 ga watan Disamba dakaru sun samu bayanan sirrin da suka nuna cewa za a kai hari ƙauyen Gidan-Saki da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna.
“Mayar da martani na nan-take da dakarunmu suka yi ya tilasta wa masu aikata laifukan su yi watsi da abin da suka yi niyyar yi kuma suka janye zuwa dazukan da ke kusa. Dakaru na amfani da ababen da ake buƙata wajen kama waɗanda ake zargin da ke tserewa,” in ji sanarwar.
A wani labari makamancin wannan, dakarun da aka tura Jengre a Jihar Filato sun yi wani kwanton-ɓauna bayan an yi garkuwa da mutum biyu a ƙauyen Rimi da ke gundumar Jere, a ƙaramar hukumar Bassa, in ji sanarwar.
Dakarun sun yi wani kwanton-ɓauna da aka tsara da kyau a kan hanyar da ɓarayin za su wuce. Kuma suna haɗuwa aka fara musayar wuta, lamarin da ya tilasta wa masu garkuwa da mutanen su ƙyale waɗanda suka yi garkuwa da su kuma suka tsere.
Sanarwar ta ce ababen da aka ƙwace daga gare su sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 ɗaya da magazine ɗaya da harsasai 13.
Ta ƙara da cewa waɗanda aka kuɓutar daga masu garkuwa da mutanen an yi musu tambayoyi kana aka haɗa su da iyalansu.















