Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce gwamnatinsa na da isassun kuɗaɗe da za su ba ta damar ci gaba da yaƙin da take yi da Iran har zuwa ƙarshen watan Janairu, inda ya ƙara da cewa zai iya kawo ƙarshen rikicin a duk lokacin da ya ga dama.
A wata hira da jaridar New York Post ta wallafa a ranar Talata, Trump ya kuma soki 'yan jam'iyyar Democrat a Majalisar Dokokin Amurka, yana mai gargaɗin cewa yunƙurinsu na takaita yaƙin na iya sauya abin da ya kira nasarar Amurka zuwa rashin nasara.
“Za su mayar da cikakkiyar nasararmuu zuwa rashin nasara,”in ji Trump, yana mai ikirarin cewa an lalata rundunar ruwan Iran, da rundunar sojin sama da tsarin kariyar sararin samaniyarta, tare da kashe shugabanninta.
Da aka tambaye shi ko za a iya takaita zaɓin da gwamnatinsa ke da shi na yaƙin idan 'yan Democrat suka karɓi iko da Majalisa a watan Janairu, Trump ya ce gwamnatinsa na da isassun kuɗaɗen da za su ba ta damar ci gaba da ayyukan soji har zuwa lokacin.
“Har zuwa ƙarshen watan Janairu, muna da isassun kuɗaɗe,” kamar yadda ya shaida wa jaridar.
Haka kuma Trump ya jaddada cewa Amurka za ta iya kawo ƙarshen yaƙin a duk lokacin da ta ga dama, yana mai cewa: “Za mu iya kawo ƙarshen wannan yaƙi a duk lokacin da muka so.”
Sannan ya taɓo batun yin magana kan yiwuwar sauya gwamnatin Iran, inda ya bayyana hakan a matsayin abu mai yiwuwa, amma ya ce ba wannan ne babban burinsa ba.
“Abin da kawai nake so shi ne kada Iran ta mallaki makamin nukiliya. Ban taɓa goyon bayan sauya gwamnati ko adawa da hakan ba. Wannan ba shi ne abin da na sanya a gaba ba,” in ji Trump.












