Tafiya zuwa wata ƙasa kan ƙunshi sauka a filayen jiragen sama daban-daban domin sauya jirgi kafin isa inda mutum ya dosa. Sai dai akwai wasu abubuwa da matafiya ke buƙatar la'akari da su fiye da lokacin tashin jirgi ko tsawon tafiya, musamman idan wurin da za su sauka yana da yanayin muhalli da zai iya shafar lafiyarsu.
Wannan shi ne saƙon da gwamnatin Nijeriya ke son isarwa ga ’yan ƙasar da ke shirin bi ta birnin Addis Ababa na Habasha, musamman waɗanda ke sauka a filin jirgin birnin domin sauya jirgi zuwa wasu ƙasashe.
A wani sabon gargaɗin tafiye-tafiye da ta fitar a watan Nuwamban 2026, Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta ce ofishin jakadancinta da ke Addis Ababa ya samu rahoton mutuwar ’yan Nijeriya 16 da suka sauka a birnin a lokuta daban-daban cikin shekarar nan.
A cewar ma’aikatar, ana danganta rasuwarsu da matsalolin lafiya da ka iya kasancewa da alaƙa da tsayin muhallin da filin jirgin yake.
Filin jirgin saman Bole International Airport na Addis Ababa yana da tsayin kusan mita 2,355 daga matakin ruwan teku, wato kimanin kilomita 2.3. Wannan tsayin na iya shafar lafiyar wasu matafiya, musamman waɗanda ke fama da wasu cututtuka.
A sauƙaƙe, kasancewa a irin wannan muhalli yana kama da hawan tsauni mai tsayi, inda yanayin iskar oxygen ya bambanta da wanda mutum ya saba samu a wuraren da suke kusa da matakin ruwan teku.
Wannan ne ya sa gwamnatin Nijeriya ta nuna damuwa, tare da buƙatar ’yan ƙasar da ke bi ta birnin su yi taka-tsantsan.
Yaya tsayin muhalli ke shafar lafiyar mutum?
Lokacin da mutum ya samu kansa a muhalli mai tsananin tudu sama da inda ya saba rayuwa, iskar oxygen da jikinsa ke samu a duk lokacin da ya ja numfashi kan ragu.
Wannan na nufin jiki na iya samun ƙarancin iskar da yake buƙata domin gudanar da ayyukansa yadda ya kamata. Hakan kuma na iya sa zuciya da huhu su ƙara ƙoƙari wajen samar da iskar oxygen da sauran sassan jiki ke buƙata.
Ga mutane da dama masu ƙoshin lafiya, jiki kan iya sabawa da wannan yanayi a hankali. Sai dai ga wasu, musamman waɗanda ke fama da cututtukan da suka daɗe suna damunsu, ƙarancin oxygen na iya haifar da matsalolin lafiya.
Mutanen da ke fama da cututtukan zuciya da na hanyoyin numfashi na cikin waɗanda suka fi fuskantar haɗari, saboda jikinsu na iya kasancewa yana fama da wahalar samun iskar oxygen da ta wadatar domin gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Duk da haka, gargaɗin gwamnatin Nijeriya bai tabbatar da cewa tsayin birnin Addis Ababa ne ya haddasa dukkan rasuwar da aka ruwaito ba. Sai dai ya jaddada muhimmancin mutanen da ke fama da wasu cututtuka su nemi shawarar likita kafin yin tafiyar da za ta ratsa ta birnin.
Waɗanne matakai ya kamata matafiya su ɗauka?
Abu na farko shi ne matafiya su fahimci yanayin lafiyarsu, da kuma yadda kasancewa a wuraren da suke da tsananin tudu zai iya shafar su.
Waɗanda ke fama da cututtukan da ka iya jefa su cikin haɗari ya kamata su tuntubi likitocinsu domin samun shawarwarin da suka dace kafin sayen tikitin jirgi ko fara tafiya.
Haka kuma, yana da muhimmanci su samu cikakken bayani game da yanayin wuraren da za su bi, tare da yin shirin da ya dace domin rage yiwuwar fuskantar matsalolin lafiya yayin tafiya.
Gwamnatin Nijeriya ba ta hana ’yan ƙasar zuwa Addis Ababa ko amfani da birnin a matsayin wurin sauya jirgi zuwa wasu ƙasashe ba. Abin da take jaddadawa shi ne, fasinjojin da ke da matsalolin lafiya da ka iya jefa su cikin haɗari su yi taka-tsantsan tare da neman shawarwarin da suka dace kafin tafiya.
A ƙarshe, muhimmin saƙon gargaɗin shi ne cewa kafin mutum ya fara tafiya, bai kamata ya yi la'akari da inda zai je kawai ba. Yana da kyau ya fahimci yanayin wuraren da zai bi, haɗarin da lafiyarsa za ta iya fuskanta da kuma matakan kariya da ya kamata ya ɗauka.












