| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro, ya ba da umarnin ɗaukar ƙarin dubban jami'an tsaro
Shugaba na Nijeriya Tinubu ya kuma buƙaci majalisar dokokin kasar ta sake duba dokokin da za su bai wa jihohi damar kafa ‘yan sanda, ya kuma yi kira ga cibiyoyin addini da su nemi kariya a lokacin taruka.
Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro, ya ba da umarnin ɗaukar ƙarin dubban jami'an tsaro
Shugaba Tinubu ya bayyana matakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba
27 Nuwamba 2025

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar tare da umurtar sojoji da ‘yan sanda su dauki karin dubban jami’ai don magance munanan matsalolin tsaro a fadin kasar.

Shugaba Tinubu ya bayyana matakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Tinubu ya ce rundunar ‘yan sanda za ta ɗauki ƙarin jami’ai 20,000, inda yawansu zai ƙaru zuwa 50,000, sannan ya ba da izinin amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima a matsayin wuraren bai wa sabbin ‘yan sandan horo.

Ya kuma bayar da umarnin tura ‘yan sandan da aka janye daga gadin manyan mutane wuraren da ake fama da rikici bayan sake horas da su.

Shugaban ya kuma bai wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) izinin tura ƙwararrun masu gadin daji cikin dazuka, tare da ɗaukar ƙarin ma’aikata domin fatattakar miyagun da ke boye a cikin dazuzzukan. "Mugaye ba za su ƙara samun wuraren ɓuya ba," in ji Tinubu a cikin sanarwar.

‘Yan sandan jihohi

Matakan sun biyo bayan hare-haren baya bayan nan a jihohin Kebbi, Borno, Zamfara, Niger, Yobe da Kwara, inda aka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da ɗaruruwa.

Tinubu ya buƙaci majalisar dokokin kasar ta sake duba dokokin da za su bai wa jihohi damar kafa ‘yan sanda, ya kuma yi kira ga cibiyoyin addini da su nemi kariya a lokacin tarukan.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta taimaka wa duk wata jiha da ta kafa rundunar tsaro don kare jama’a daga ‘yan ta’adda.

Sannan ya yi kira ga jihohi su sake tunani kan kafa makarantun kwana a wuraren masu nisa da ba su da cikakken tsaro.

Ya kuma bukaci kungiyoyin makiyaya da su rungumi kiwon killace, tare da mika makaman da ba su dace su dauka ba, saboda kawo karshen rikici da manoma.

Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro kan ceto ‘yan mata 24 a Kebbi da kuma masu ibada 38 a jihar Kwara, tare da shan alwashin kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su ciki har da ɗaliban da aka sace a jihar Neja.

“Ina jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan’uwansu tare da jinjina wa jajirtattun sojojinmu, ciki har da Birgediya-Janar Musa Uba,” in ji Tinubu.

Najeriya dai na fuskantar tashe-tashen hankula daga ‘yan ta’adda, da 'yan bindiga da kuma fadace-fadacen kabilanci da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu a 'yan shekarun nan.