6 Maris 2026
Hukumomi a Saudiyya sun ce sun kakkaɓo makamai masu linzami uku da Iran ta harba wani sansanin sojin sama.
“An kakkaɓo makamai masu linzami uku tare da lalata su bayan sun nufi Sansanin Sojin Sama na Yarima Sultan,” a cewar wani saƙo da ministan tsaron Saudiyya ya wallafa a shafin X.
