Jam'iyyar Union for the Republic party (UNIR) ta su Shugaba Gnassingbe ta lashe kujeru 108 daga cikin 113 na sabuwar majalisar dokokin ƙasar, a cewar sakamakon da hukumar zaɓen Togo ta fitar ranar Asabar. / Hoto: Reuters

Jam'iyya da ke mulki a Togo ta samu gagarumar nasara a zaɓen majalisar dokoki da aka gudanar ranar 29 ga watan Afrilu, a cewar hukumar zaɓen ƙasar, bayan gyaran fuskar da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar wanda 'yan hamayya suka ce zai bai wa Shugaba Faure Gnassingbe ci gaba da mulki.

Jam'iyyar Union for the Republic party (UNIR) ta su Shugaba Gnassingbe ta lashe kujeru 108 daga cikin 113 na sabuwar majalisar dokokin ƙasar, a cewar sakamakon da hukumar zaɓen Togo ta fitar ranar Asabar.

Sabon kundin tsarin mulki da majalisar dokoki ta amince da shi a watan Afrilu ya bai wa Gnassingbe damar zama shugaban majalisar ministoci, muƙamin da zai kasance tamkar na firaiminista da shugaban jam'iyya mai mulki ne kawai zai riƙe shi.

Gnassingbe ya kwashe kusan shekaru 20 a kan mulki bayan ya gaji mahaifinsa Gnassingbe Eyadema, wanda ya yi kusan shekaru arba'in yana mulkin ƙasar wadda ke tsakanin Benin da Ghana.

Sabon kundin tsarin mulkin Togo

Jam'iyyun hamayya sun bayyana gyaran fuskar da aka yi wa tsarin mulkin Togo a matsayin wani "juyin mulki" da aka yi domin bai wa Gnassingbe damar tsawaita wa'adin mulkinsa.

Sai dai masu goyon bayan UNIR sun ce gyaran fuskar zai ƙarfafa dimokuraɗiyyar e Togo yadda za a dama da kowa. Tuni dai Gnassingbe, mai shekara 57, ya lashe zaɓuka huɗu na shugaban ƙasa, ko da yake 'yan hamayya sun ce an tafka maguɗi.

Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasar ta ƙaurace wa zaɓen majalisar dokokin da akar gudanar a shekarar 2018, inda ta yi zargin an yi maguɗi.

A ƙarƙashin sabon kundin tsarin mulkin Togo, yanzu shugaban ƙasar zai kasance na je-ka-na-yi-ka da 'yan majalisar dokoki za su zaɓa, ba al'ummar ƙasar ba, don yi wa'adin mulki na shekara huɗu.

AFP