| Hausa
WASANNI
2 MINTI KARATU
Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba— Poseiro
An cire Yusuf ne a wasan Nijeriya da Equitorial Guinea bayan ya ji ciwo ranar Lahadi, kuma an tashi wasan 1-1.
Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba— Poseiro
Ranar Lahadi ne dai Alhassan Yusuf ya fara buga wa Nijeriya wasa mai muhimmanci : Hoto/GettyImages / Others
17 Janairu 2024

Kocin tawagar Nijeriya ta Super Eagles, Jose Poseiro ya tabbatar da cewar dan wasan tsakiya na kunfgiyar, Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) da ake yi a Ivory Coast.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ambato Poseiro ranar Laraba yana tabbatar da cewa sai a karawar da Nijeriya za ta yi da Guinea Bissau ne dan wasan zai buga wa Nijeriya.

Alhassan Yusuf, wanda ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp da ke Belgium, ya ji ciwo ne a wasan farko da Nijeriya ta buga da Equatorial Guinea a gasar AFCON.

An cire Yusuf ne a wasan Nijeriya da Equitorial Guinea bayan ya ji ciwo ranar Lahadi, kuma an tashi wasan 1-1.

Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, kocin na Nijeriya ya tabbatar da cewa Victor Osimhen zai buga wa Super Eagles a karawarsu da Eelephants na Ivory Coast.

MAJIYA:TRT Afrika