A watan Yulin bara ne Nicolas Jackson ya zo Chelsea daga Villareal ta Sifaniya. / Hoto: AFP

Gwarzon tsohon ɗan wasan Chelsea, kuma tsohon manajan kulob ɗin da ke Landan, wato Frank Lamfard, ya soki ɗan wasan gaba na Chelsea kan gaza cin ƙwallaye da ya samu damar ci a wasan da suka yi rashin nasara ranar Asabar.

Lamfard ya ce Nicolas ya samu fasin ɗin ƙwallaye da dama, waɗanda aka ajiye masa kawai sai dai ya zura su raga, amma ya gaza cin ko da guda.

Rashin cin ƙwallon da Chelsea ta yi, shi ya ba wa Man City damar yin nasara a wasan, bayan da ɗan wasansu Bernardo Silva ya zura ƙwallo ɗaya tilo a minti na 84.

Nicolas Jackson, ɗan shekara 22 wanda ɗan asalain Senegal ne ya zo Chelsea a watan Yulin 2023, daga ƙungiyar Villareal ta Sifaniya kan kuɗi Fam miliyan 35, da kwantiragin shekara takwas.

A makon da ya gabata an zargi Nicolas da rashin nuna ɗa'ar wasa, bayan da shi da Noni Madueke suka yi ta ƙoƙarin karɓe ƙwallo daga abokin wasansu, Cole Palmer domin su buga ƙwallon ɗurme, a wasan da Chelsea ta doke Everton da ci 6-0.

A wasan na Asabar da aka buga a katafaren filin wasa na Wembley a birnin Landan, Chelsea ƙarƙashin koci Mauricio Pochettino sun ɓarar da damarmaki da yawa, a wasan da masu sharhi suke ganin Chelsea ce ya kamata ta yi galaba.

Wasan ya zo ne kwanaki uku kacal bayan da ƙungiyar Man City ta sha kaye a hannun Real Madrid, a wasansu na matakin kwata-fainal a gasar kofin Zakarun Turai.

Rashin nasarar City a wancan wasan ya sa ake ganin sun zo buga wasa da Chelsea cike da jimamin da ake ganin zai bai wa Chelsea damar yin nasara kansu. Sai dai bayan gazawar Chelsea na zura ko da ƙwallo ɗaya, CIty ta ci wasan da 1-0.

A maraicen yau Lahadi ne Man United za ta kara da Coventry a ɗaya ɓangaren na wasan dab da na ƙarshe na cin kofin FA na bana, domin fitar da wanda zai kece raini da Man City a wasan ƙarshe na gasar da za a buga a ranar 25 ga watan Mayu.

TRT Afrika