Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan zai je birnin Alkahira domin halartar Taron Majalisar Ministocin Harkokin Wajen Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa (AL) karo na 162 da za a fara ranar Talata.
Ana sa ran Fidan zai tattauna muhimman batutuwan da suka shafi yankin, tare da mayar da hankali musamman kan Gaza, da kuma karfafa dangantaka tsakanin Turkiyya da kungiyar kasashen Larabawa.
Jawabin nasa zai ba da haske kan rawar da Turkiyya ke takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a cikin tarihinta na kai tsaye da kuma fadin yankin baki daya, yana mai jaddada karuwar gudunmawar da Ankara ke bayarwa ta hanyar ingantattun manufofin kasashen waje.
Ana kuma sa ran jawabin na Fidan zai jadada muhimmancin Falasdinu da sauran muhimman batutuwan yankin, wadanda ke ci gaba da kasancewa kan ajandar manufofin ketare na Turkiyya.
Dangantakar da Turkiyya ke samu cikin sauri da ƙasashen Larabawa, ba wai kawai ta taimaka wajen samar da hanyoyin magance kalubalen yankin ba, har ma ta bude wasu sabbin damarmaki na hadin gwiwa da samun moriyar juna.
Turkiyya na ba da fifiko wajen bunkasa alakar hukumomi da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da inganta hadin kai kan muhimman batutuwa.
Haɓaka dangantakar Turkiyya da Ƙasashen Larabawa
Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a alakar Turkiyya da kungiyar kasashen Larabawa sun hada da ziyarar da ministan harkokin wajen kasar ya kai birnin Alkahira a watan Oktoban shekarar 2023, inda ya gana da babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit.
Kwanan nan, an gudanar da shawarwarin siyasa a Ankara a watan Fabrairun 2024 tsakanin Mataimakin Ministan Harkokin Waje Ambasada Ahmet Yildiz da Mataimakin Babban Sakatare Janar na AL Ambasada Hossam Zaki, wanda daga baya ya halarci taron diflomasiyya na Antalya.
Tun a shekara ta 2003 ne aka kulla yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya da kuma sakatariyar kungiyar a shekara ta 2004.
A shekarar 2007 ne aka kafa yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Larabawa, inda ta kara karfafa alaka.
A shekara ta 2011, firaministan lokacin kuma a yanzu shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan shi ma ya gabatar da jawabi a wurin bude taron majalisar, inda ya jaddada dauriyar Turkiyya ta yi kan diflomasiyyar kasashen Larabawa.
Sanarwar da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi a yayin Taron Ƙolin Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai ta OIC da Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa a watan Nuwamba na shekarar 2023 na nan daram a yayin da ake ci gaba da yakin Isra'ila a Gaza.
Shugaba Erdogan ya ce "Mun tabbatar da cewa ba zai yiwu ba a samu zaman lafiya a yankin tare da yin watsi da batun Falasdinu ko kuma yin watsi da hakkin al'ummar Falasdinu."
"Muna jaddada cewa shirin samar da zaman lafiya na kasashen Larabawa, wanda Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai da Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa ke mara wa baya, wani muhimmin nuni ne ga hakan," in ji shi.
Yakin kisan kare dangi na Isra'ila a Gaza ya kashe Falasdinawa kusan 41,000 - akasari mata da kananan yara.