Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi jawabi ga Babban Taron MDD karo na 78 a birnin New York. Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadi mai karfi a kan yiwuwar amfani da karfin soji a kan Jamhuriyar Nijar inda ya jaddada hadarin hakan kan ta'azzara rashin zaman lafiya a kasar da ma yankin Sahel baki daya.

Erdogan ya fadi hakan ne a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ke gudana a birnin New York na Amurka a ranar Talata, inda ya ce Sahel na fuskantar manyan barazana na siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da kuma na tsaro.

"Duk wani matakin amfani da karfin soji a Nijar ka iya sanya kasar da ma yankin gaba daya cikin rashin tabbas," ya yi gargadi. "Muna fatan Nijar, wacce ke fama da matsaloli a kwanan nan, ta cimma wata matsaya ta mayar da dimokuradiyya kuma ba tare da bata lokaci ba."

A ranar 26 ga watan Yuli ne Nijar ta shiga rudani bayan da Janar Abdourahamane Tchiani, wani tsohon kwamanda na rundunar da ke tsaron fadar shugaban kasa ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da Mohamed Bazoum.

'Ba za a lamunci ƙin jinin Musulunci ba'

Kazalika a wasjen taron Shugaba Erdogan ya yi magana a kan alamun ƙin jinin baƙi da wariyar launin fata da ƙin jinin Musulunci da ya ce suna ƙaruwa tare da zama wani sabon rikici, inda suka kai matakin da ya kamata a damu a cikin shekara ɗayar da ta wuce.

Da yake bayani kan yadda kalaman ƙiyayya, shugaban ya ce nuna ƙiyayya ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba na ɓata ran mutane a kowane lungu da saƙo na duniya, shugaban Turkiyyan ya koka, inda ya ce ƴan siyasar da ke goyon bayan irin wannan tsari suna wasa da wuta ne.

"Munanan ayyukan wulakanta Kur'ani da ake yi a Turai da sunan ƴancin faɗin albarkacin baki abu ne da zai iya jawo matsala a nan gaba," shugaban kasar ya fada.

Shugaba Erdogan ya jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan shirye-shoryen yaki da ƙin jinin Musulunci a dukkwan kafofi, musamman a MDD fa Kungiyar Hadin kai kan Tsaro ta Turai (OSCE) da kuma Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai (OIC).

Shugaban kasar ya kuma yi kira ga shugabannin kasashen duniya wadanda ya ce sun yi biris da irin wadannan hare-hare a kan abubuwa masu tsarki maimakon goyon bayan kokarin Turkiyya.

Erdogan ya yi wadannan kalamai ne sakamakon kona Kur'ani da aka yi ta yi a jere musamman a wasu kasashenarewacin Turai, wadanda yawanci an yi su karkashin kariyar da ƴan sanda suka bai wa masu yin.

Batun Azabaijan

"Karabakh yankin kasar Azabaijan ne, ba za a taba amincewa da kakaba duk wani matsayi ba," in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, duk a jawabin da ya gabatar a wajen Babban Taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Dangantakar Baku da Yerevan ta yi tsami tun 1991 a lokacin da Armeniya ta mamayi Karabakh, yankin da kasashen duniya suka amince da na Azabaijan ne, da yankuna bakwai da ke kusa da wajen.

Azabaijan ta kubutar da garuruwa da dama, kauyuka da matsugunai daga mamayar Armeniya a arangamar kwanaki 44 da aka fafata a bazarar 2020. Yakin ya zo karshe bayan tsagaita wutar da aka cimma tare da shiga tsakanin da Rasha ta yi.

Rikici tsakanin kasashen biyu ya ci gaba, duk da tattaunawar da ake kan yi game da kulla yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa.

Hanyar Zangezur

Turkiyya na goyon bayan matakan da Azabaijan ke dauka na kare martabar iyakokinta, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, inda ya kara da cewa ya kamata Armeniya ta cika alkarurrukan da ta yi, musamman bude hanyar Zangezur. Ya bayyana hakan a wajen Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

Hanyar Zangezur ta hada Azabaijan da yankinta na Nakhchivan mai cin gashin kansa da ba shi da iyaka da teku. A taswirance, Armeniya ta yanki Nakhchivan daga yankin kasar Azabaijan.

Hanyar na bayar da dama ga mutane da kayayyaki su kai su komo tsakanin Azabaijan da Nakhchivan inda suke bi ta lardin Syunik na Armeniya.

TRT World