| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Turkiyya ta shiga sabon kawance na wasu kasashen Afirka
Inganta hadin kai da kungiyoyin shiyyoyi a Afirka na daga abubuwan da Turkiyya ta bai wa fifiko, in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar.
Turkiyya ta shiga sabon kawance na wasu kasashen Afirka
ICGLR na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ci-gaba da tsaro/ Hoto: Rueters / Others
24 Mayu 2023

Turkiyya ta shiga kungiyar kawaye da wakilai na musamman na Babban Taron Kasa da Kasa Kan Yankin Manyan Tafkuna (ICGLR) daga watan Mayu, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar.

A sanarwar da ma’aikatar ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa “Manufarmu ta kawance da Afirka na da babban matsayi a kundin manufofofin harkokin waje kan ci-gaba da gina dan adam na Turkiyya. A wannan gaba, inganta alakarmu da kungiyoyin shiyyoyi a nahiyar Afirka na daga abubuwan da muka bai wa fifiko.”

Sanarwar ta kara da cewa ICGLR na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, ci-gaba da tsaro.

Ma’aikatar ta ce “Karbar mu a wannan kungiya za ta kawo sabon salo ga manufarmu ta hadin kai da Afirka, hadin kanmu da Yankin Manyan Tafkuna, sannan a kulla dangantaka ta kusa da ICGLR, gami da tallafawa ayyukan kungiyar.”

Manufar ICGLR ita ce tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen Angola, Burundi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Kongo, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Kenya, Uganda, Ruwanda, Sudan ta Kudu, Sudan, Tanzaniya da Zambiya.

MAJIYA:TRT World