Uwargidan shugaban Turkiyya ta ce kasarta za ta ci gaba da bai wa Falasdinawa gudunmawa a halin da suke ciki. / Hoto:AA

Uwar gidan Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta nuna matukar damuwarta kan irin hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Falasdinawa, inda ta ce Ankara za ta ci gaba da kokari wurin bayar da duk wata gudunmawa ga Falasdinawa.

“A yau, sakamakon hare-haren Isra’ila a yankunan Falasdinawa da ta mamaye musamman Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, muna shaida irin bala’in da yaki yake da shi kan mata da yara. A daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da tayar da bama-bamai da harba harsasai kan farar hula a Falasdinu, ra’ayinmu kan hakan na tattare da ban tsaro da kuma damuwa,” in ji Erdogan a wata hira ta musamman da aka yi da ita a ranar Litinin.

Isra’ila ta jawo dubban mutane sun rasu da kuma samun raunuka inda suka kai hari kan makarantu da wuraren bauta da kan kayayyakin agaji, kamar yadda mai dakin Erdogan din ta bayyana.

Ta kara da cewa Isra’ilar ta sa asibitoci 18 cikin 35 da ke Gaza ba su aiki bayan hare-haren da ta kai musu, daga ciki har da asibitin hadin gwiwa na Turkiyya da Falasdinu.

“Abin takaicin shi ne babu wani amintaccen wuri a yankin Gaza mai mutum miliyan 1.5 wadanda aka raba da muhallansu da karfi da yaji. Akwai mata masu ciki da iyaye mata da yara kanana da kuma yara masu bukata ta musamman a cikin wadannan mutanen. Za ku iya tunanin irin wahalar da suke sha domin fama da wannan matsala ta yaki da raba su da muhallansu?” in ji ta.

Ta bayyana cewa babu bambanci tsakanin yaran Falasdinawa da kuma sauran yara da ke Ukraine da Turai da Amurka da Turkiyya ko sauran kasashe inda ta ce “Ko wane yaro yana da ‘yanci ya kasance cikin aminci a gida, da kuma samun nagartaccen ilimi da kiwon lafiya a ko ina aka haife su.”

TRT World