Amma kwanakin baya bayan nan Hezbollah ta ƙara ƙaimi wurin kai wa Isra'ila hari. / Hoto: Reuters

1221 GMT –– Hezbollah ta kai wa Isra'ila hare-hare da jirage marasa matuƙa

Kungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta ce ta kai hare-hare a sansanoni biyu na Isra'ila da ke arewacin ƙasar domin yin ramuwar gayya kan kisan da Isra'ila ta yi wa wani mayaƙinta mai "muhimmanci".

Tun da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza bayan harin ba-zata da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, kusan kullum ana samun musayar wuta tsakanin Hezbollah da sojojin Isra'ila a kan iyakar ƙasar.

Amma kwanakin baya bayan nan Hezbollah ta ƙara ƙaimi wurin kai wa Isra'ila hari.

Hezbollah ta ƙaddamar da "hari ta sama a sansanoni biyu na Isra'ila d ke arewacin Acre ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da ke fashewa," in ji wata sanarwa da ta fitar, ko da yake Isra'ila ta ce jiragen ba su sauka inda aka aika su ba.

0651 GMT —Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 34,183

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 34,183 tun lokacin da ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza kwanaki 200 da suka wuce zuwa yanzu, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta yankin.

Cikin mutanen da suka mutu, har da mutum 32 ta dakarun Isra'ila suka kashe a awanni 24 da suka gabata, in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa Isra'ila ta kuma jikkata Falasɗinawa aƙalla 77,143 a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Dakarun Isra'ila sun kai hari a Masallacin Al Taqwa da ke sansanin ƴan gudun hijira na Al Bureij da ke Deir al Balah, Gaza. / Hoto: AA

0330 GMT — Sojin ruwan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a Gaɓar Tekun Gaza da kai hare-hare ta sama a arewacin ƙasar

Jiragen yakin sojin Isra'ila sun kai hari a Gabar Tekun Al Zawaida da Deir al Balah, da Al Nusairat yayin da yankunan arewacin Gaza suka fuskanci hare-haren wuce gona da iri, wanda ya yi sanadiyar hallaka da jikkata wasu fararen-hula, tare da lalata gidaje da kadarori, kamar yadda kafar yada labaran Falasdinu ta ce.

Wakilan kamfanin dillancin labarai na WAFA sun ruwaito cewa, bayan shafe kwanaki 200 na hare-haren Isra'ila, jiragen yakin sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta a Gabar Tekun Al Zawaida da Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza a safiyar yau Talata. Hakazalika jiragen yakin sojin Isra'ila sun yi luguden wuta kan Gabar Tekun Al Nusairat.

Sojojin Isra'ila sun kai hari a arewacin sansanin Al Nusairat da ke tsakiyar Gaza, yayin da jiragen yakin suka kai farmaki kan titin Thirty Streer da ke tsakiyar birnin.

Sojin ruwan Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a Gaɓar Tekun Gaza .  / Hoto: Reuters

2200 GMT — UNRWA ta yaba da nazari mai zaman kansa wanda ya ƙaryata ikirarin Isra'ila

Hukumar da ke kula da ayyukan jinƙai na Falasɗinawa masu gudun hijira ta MDD, UNRWA ta yi maraba da sakamakon wani nazari mai zaman kansa kan yadda kungiyar ke bin ƙa’idar ba da ‘yancin kai da tsohuwar ministar harkokin kasashen Turai da harkokin waje, Catherine Colonna ta yi, wanda ya tabbatar da cewa kungiyar na da tsare-tsare don magance zarge-zargen da ake yi na nuna bacin rai.

"Muna maraba da sakamakon binciken mai zaman kansa na UNRWA da @MinColonna ta yi. Ya nuna cewa muna da tsarin kiyaye dokokinmu - da muhimmiyar ka'idar jinƙai - kuma muna yin aiki lokacin da aka samu sabani," in ji kungiyar a shafin X.

"Wannan yana da mahimmanci ga ayyukan agajin da muke yi a Gaza da kuma ayyukanmu a fadin yankin."

Shugaban hukumar @UNRWA, Philippe Lazzarini, shi ma ya yi maraba da sakamakon nazarin sannan ya kara da cewa za su aiwatar da shawarwarin ba tare da ɓata lokaci ba.

"Wannan zai karfafa kokarinmu da mayar da martani a lokacin daya daga cikin mawuyacin lokaci a tarihin al'ummar Falasdinu," in ji shi a X.

TRT Afrika da abokan hulda