Falasɗinawa da suke tserewa daga Rafah saboda hare-haren Isra'ila sun kafa tantuna tsakanin Deir al Balah da Khan Younis a Gaza ranar 21 ga Mayu, 2024. / Hoto: AA

0924 GMT –– Sojojin Isra’ila sun faɗaɗa farmakin da suke kai wa birnin Rafah, a kudancin Gaza, yayin da Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta.

Shaidu sun faɗa wa kamfanin dillacin labarai na Anadolu cewa sojojin na Isra’ila sun kuma faɗaɗa hare-harensu zuwa farfajiyar Philadelphi, wani waje tsakanin Gaza da Masar, yayin da dakarun Isra’ila suka dangana da yammacin sansani ‘yan gudun hijira na Yibna a tsakiyar Rafah.

Farfajiyar ta Philadelphi wani waje ne mai nisan kilomita 14 da aka ware cewa ba za a kutsa cikin ba, a lokacin da aka saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Masar a 1979.

A sabon kutsen da sojojin suke yi a yankin Rafah, dakarun Isra’ila sun ƙwace ikon fiye da rabin farfajiyar ta Philadelphi har zuwa kusa da iyakar Masar.

Falasɗinawa da suka bar gidajensu sun yi layi don samun ruwa a wani sansanin 'yan gudun hijira da yammacin Deir al-Balah a Gaza ranar 21 ga Mayu, lokcin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankunan da aka mamaye. / Hoto: AFP

0100 GMT — MDD ta dakatar da raba abinci a Rafah saboda ya ƙare

Majalisar Ɗinkin Duniya ta dakatar da raba kayan abinci a birnin Rafah da ke kudancin Gaza saboda rashinsa da kuma rashin tabbas na tsaro a yankin sakamakon hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kai wa.

MDD ta yi gargaɗi cewa ayyukanta na bayar da agajin jinƙai a yankin suna dab da durƙushewa.

Tun da farko, wani jami'in MDD ya ce sun dakatar da kai kayan agaji Gaza ta hanyar wata ƙungiya tun ranar Asabar da ta gabata.

Dubban Falasɗinawa ne suke ta tserewa daga Rafah a wani yanayi na ruɗani tun makonni biyu da suka gabata, inda suke neman mafaka a sabbin tantuna da wuraren da ke cike da jama'a saboda hare-haren da Isra'ila ta matsa ƙaimi wurin kai musu.

Akwai kimanin mutum 400,000 a Rafah bayan sama da mutum 900,000 sun fice daga yankin, a cewar COGAT, wato ofishin sojojin Isra'ila da ke sanya ido kan Falasɗinawa fararen-hula.

2237 GMT — Ireland na shirin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yancin kanta

Gwamnatin Ireland tana shirin bayar da sanarwar amincewarta da yankin Falasɗinu a matsayin ƙasa mai 'yancin kanta, duk da yake Isra'ila ta yi matuƙar adawa da wannan matakin, a cewar wata majiya da ke da masaniya game da lamarin.

Ƙasashe mambobin Tarayyar Turai da suka haɗa da Ireland, Sifaniya, Slovenia da Malta a makonnin baya bayan nan sun bayyana aniyarsu ta amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa, wataƙila a taron haɗin-gwiwa, suna masu cewa bai wa yankin na Falasɗinu 'yanci shi ne kaɗai zai kawo dauwamammen zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Wannan yunƙuri na zuwa ne a yayin da Isra'ila ke ƙara shan matsin lamba daga ƙasashen duniya domin ta daina kisan kiyashin da take yi a Gaza.

Tun shekarar 1988, ƙasashe 139 cikin 193 mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Gwamnatin Ireland ta ce matakin da za ta ɗauka na amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa zai ƙara ƙaimi a yunƙurin tabbatar da zaman lafiya da kuma samun ƙasashe biyu kowace mai 'yancin kanta.

An sanya wa wani yaro filasta a Asibitin Al-Aqsa Martyrs bayan Isra'ila ta jikkata shi a harin da ta kai sansanin 'yan gudun hijira na Bureij da ke yankin Deir al Balah na Gaza ranar 21 ga watan Mayu, 2024. / Hoto: AA

2204 GMT — Norway ta ce 'wajibi’ ne ta kama Netanyahu idan ICC ta bayar da umarni

Norway ta zama ƙasa ta farko ta Turai da ta bayar a sanarwar cewa za ta kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaronsa Yoav Gallant idan Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta tabbatar da sammacin kama su.

Ministan Harkokin Wajen Norway Espen Barth Eide ya ce idan aka gabatar da sammacin kama Netanyahu da Gallant a madadin Kotun da ke Hague, za su bi umarninta na kama su idan mutanen biyu suka je Norway.

Wata jaridar ƙasar Norway da ake wallafawa a shafin intanet Eide ta tabbatar da cewa Netanyahu zai fuskanci yiwuwar a miƙa shi ga kotun idan ya je ƙasar Norway.

TRT Afrika da abokan hulda