| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Sojoji sun ce sun ƙwace iko da Guinea Bissau sun soke zaɓen Shugaban Ƙasa
Tun da fari hukumar zabe ta gargaɗi masu zaɓe, da 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, da ƙungiyoyin zaɓe da kuma kafofin watsa labarai game da sanar da yin taka tsan-tsan wajen sanar da duk wani sakamako.
Sojoji sun ce sun ƙwace iko da Guinea Bissau sun soke zaɓen Shugaban Ƙasa
Sojoji sun ce sun ƙwace iko da Guinea Bissau sun soke zaɓen Shugaban Ƙasa
26 Nuwamba 2025

Wasu jami'an soji a Guinea-Bissau a ranar Laraba sun dakatar da tsarin zaɓen ƙasar kuma sun ce a yanzu ƙasar tana ƙarƙashin ikonsu "har sai an samu ƙarin sanarwa."

Jami'an, waɗanda suka kira kansu "Manyan Kwamandojin Soji don Maido da Doka," sun karanta wata sanarwa a hedikwatar rundunar sojin da ke bayyana ayyukansu.

Sun sanar da dakatar da tsarin zaɓen da ake ci gaba da yi, sun soke sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da na 'yan majalisa, da kuma dakatar da shirye-shiryen kafofin watsa labarai, yayin da suka yi kira ga al'ummar ƙasar da su "kwantar da hankalinsu."

Kwace iko da sojojin suka yi ya biyo bayan rahotannin harbe-harben bindiga kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau a ranar Laraba.

Tun da fari a ranar Larabar an yi ta jin karar harbe-harbe kusa da Fadar Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau a ranar Laraba yayin da rikici ya kaure bayan zaben Shugaban Ƙasa da aka gudanar, inda 'yan takara biyu kowannensu ya ayyana samun nasara na lashe zaben, a cewar kafofin watsa labaran Faransa.

Kazallika, kafofin yada labarai na cikin gida a Gunea- Bissau sun kuma tabbatar da rahoton cewa "a daidai wannan lokacin, za ku iya jin ƙarar harbe-harbe a Bissau, ƙarar na fitowa ne daga Fadar Shugaban Ƙasa," a cewar rahoton Bantaba Radio/TV.

A ranar Litinin ne Fernando Dias, ɗan takara mai zaman kansa, da kuma magoya bayan Shugaba Umaro Sissoco Embalo suka yi ikirarin lashe zaben Shugaban Ƙasa na Guinea-Bissau da aka gudanar a ƙarshen mako yayin da al’ummar ƙasar ke jiran sakamakon.

Hukumar zaɓen ƙasar ta yi alƙawarin sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen nan da ranar Alhamis.

Hukumar ta gargaɗi masu zaɓe, da 'yan takara, da jam'iyyun siyasa, da ƙungiyoyin zaɓe da kuma kafofin watsa labarai game da sanar da yin taka tsan-tsan wajen sanar da duk wani sakamako.

Jakadan Ghana Baba Kamara, wanda kuma shi ne shugaban tawagar sa ido kan zaɓen daga Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a Guinea-Bissau a babban zaɓen da aka gudanar a ranar 23 ga Nuwamba, ya ce tsarin zaɓen ya tafi daidai.

'Yan takara goma sha biyu ne suka fafata a takarar neman kujerar shugaban ƙasa.

Tun lokacin da shugaban Embalo ya hau karagar mulki a shekarar 2020, an yi ta samu rahotanni da dama na yunƙurin juyin mulki, wani al’amari da ke nuna rirn mummunar adawa da yake fuskanta.