Wata kotu a birnin Paris ta yanke wa tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, hukuncin ɗaurin shekaru biyar a gidan yari a ranar Alhamis, bayan ta same shi da laifi kan zargin da ake masa kan cewa tsohon shugaban Libiya, Muammar Gaddafi, ya taimaka wajen daukar nauyin yakin neman zabensa na 2007 wanda ya kai shi ga nasara.
Kotun ta umarci cewa a tsare Sarkozy zuwa wani lokaci, tare da bai wa masu gabatar da kara wata daya su sanar da tsohon shugaban kasar lokacin da zai fara zaman gidan yari.
Ko da Sarkozy ya daukaka kara kan hukuncin, wannan matakin zai ci gaba da kasancewa.
Sarkozy, wanda ya musanta zarge-zargen tun farko, an tuhume shi da yin yarjejeniya da Gaddafi don samun kudin yakin neman zabe a madadin goyon bayan gwamnatin Libiya wanda ta zama saniyar-ware a duniya a lokacin.
Alkalin, wanda ya wanke Sarkozy daga wasu tuhume-tuhume ciki har da cin hanci, ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa Sarkozy ya yi irin wannan yarjejeniya da Gaddafi, ko kuma cewa kudin da aka turo daga Libiya ya shiga asusun yakin neman zabensa.
Haka kuma, alkalin ya umarci Sarkozy da ya biya tarar euro 100,000 (kimanin dala 117,000).
Shari'ar Sarkozy ita ce ta baya-bayan nan a jerin matsalolin shari'a da tsohon shugaban mai shekaru 70 ya fuskanta, wanda ya musanta dukkan zarge-zargen.
Sarkozy, wanda ya shugabanci kasar daga 2007 zuwa 2012, tuni aka same shi da laifi a wasu shari'o'i biyu daban-daban kuma aka ƙwace masa lambar yabo mafi girma ta Faransa.
Mai Shari’a Nathalie Gavarino ta ce Sarkozy, a matsayinsa na minista da shugaban jam'iyya a lokacin, ya bai wa abokan aikinsa da magoya bayansa damar kusantar hukumomin Libiya don neman tallafin kudi.
Duk da haka, hukuncin kotun bai bi bayanan masu gabatar da ƙara kan cewa Sarkozy ne ya ci gajiyar kudin yakin neman zaben ba bisa ka'ida ba.
An wanke shi daga wata tuhuma ta karkatar da kudaden jama'ar Libiya, cin hanci da kuma daukar nauyin yakin neman zabe ba bisa ka'ida ba.
Ya halarci kotun don sauraron hukuncin tare da matarsa, Carla Bruni-Sarkozy, wacce ta kasance jaruma kuma mawakiya.
Haka kuma, wasu abokan aikinsa biyu na kusa an yanke samu hukunci. Claude Gueant, wanda ya kasance na hannun damarsa, an same shi da laifin cin hanci da kuma yin jabun takardu, yayin da tsohon minista Brice Hortefeux aka yanke masa hukunci kan hada baki wajen aikata laifi.
Eric Woerth, wanda ya kasance mai kula da kudin yakin neman zaben Sarkozy na 2007, an wanke shi daga dukkan zarge-zargen.
A wani yanayi mai ban mamaki, an yanke hukuncin ne kwanaki biyu bayan mutuwar Ziad Takieddine, wani dan kasuwa dan asalin Faransa da Lebanon, wanda ya kasance babban mai zargin Sarkozy a wannan shari'a.
Takieddine, mai shekaru 75, ya yi ikirarin cewa ya taimaka wajen kai kudade har euro miliyan biyar daga Gaddafi zuwa Sarkozy da shugaban ma'aikatansa a shekarun 2006 da 2007.
Daga baya ya janye wannan ikirari kafin ya sake musanta janyewar, wanda ya haifar da bude wata shari'a kan Sarkozy da matarsa, kan zargin matsa wa wani shaida lamba.
Masu gabatar da kara sun yi ikirarin cewa Sarkozy da abokan aikinsa sun tsara wata yarjejeniya da Gaddafi a 2005 don daukar nauyin yakin neman zabensa na 2007 ba bisa ka'ida ba.
Shari'ar ta dogara ne kan bayanan tsofaffin jami'an gwamnatin Libiya guda bakwai, ziyarar Gueant da Hortefeux zuwa Libiya, canja wurin kudade, da kuma littattafan tsohon ministan man fetur na Libiya, Shukri Ghanem, wanda aka tsinci gawarsa a kogin Danube a Vienna a 2012.
Sarkozy ya fuskanci jerin matsalolin shari'a tun bayan wa'adin mulkinsa, ciki har da tuhume-tuhume kan cin hanci, rashawa, da kuma karya dokokin yakin neman zabe.
An fara yanke masa hukunci na farko kan cin hanci inda aka yanke masa hukuncin shekara daya a gidan yari.
Bugu da kari, an yanke masa hukuncin shekara daya a gidan yari - watanni shida na ainihi da sauran watanni shida a dakatarwa - a shari'ar da aka fi sani da 'Bygmalion affair' kan karya dokokin yakin neman zabe.
Sarkozy ya daukaka kara zuwa babbar kotun daukaka kara ta Faransa don kalubalantar wannan hukunci.
Baya ga matsalolin shari'a, ya rasa lambar yabo ta Legion of Honour — mafi girma a Faransa — bayan samunsa da laifin cin hanci.
Duk da matsalolin shari'a, Sarkozy, wanda ya yi suna da lakabin 'hyper-president' yayin mulkinsa, har yanzu yana da tasiri da farin jini a bangaren masu tsatsauran ra’ayi a siyasar Faransa, kuma an ce yana yawan ganawa da Shugaba Emmanuel Macron.