NIJERIYA
4 minti karatu
Dalilan NUPENG na yin yajin aiki a kan Matatar Dangote
Shugaban ƙungiyar NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana ranar Lahadi cewa ƙungiyar za ta ci gaba da  yajin aikin zuwa ƙarshen tattaunawar ƙungiyar da gwamnati ranar Litinin.
Dalilan NUPENG na yin yajin aiki a kan Matatar Dangote
Dalilan NUPENG na yin yajin aiki a kan Matatar Dangote / Reuters
8 Satumba 2025

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan da ke dakon man fetur da Gas a Nijeriya (NUPENG) ta ce lallai sai ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani daga ranar Litinin duk da sa bakin gwamnatin tarayyar ƙasar wajen ba su haƙuri su janye yajin aikin.

Shugaban ƙungiyar NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana a ranar Lahadi cewa ƙungiyar za ta ci gaba da yajin aikin zuwa ƙarshen tattaunawar ƙungiyar da gwamnati a ranar Litinin.

A ranar Jumma’a ne dai ƙungiyar ta bayyana cewa za ta fara yajin aikin ranar 8 ga watan Satumba, lamarin da zai iya janyo rashin mai a ƙasar.

Ta ce za ta hana mambobinta dakon mai a faɗin ƙasar daga ranar Litinin idan har lamarin bai sauya ba.

Amma mene ne ya sa ƙungiyar ta tsunduma cikin yajin aiki?

Ta ɗauki matakin ne sakamakon shirin Matatar Man Dangote na shigo da tankokin dakon mai masu amfani da iskar gas na CNG guda 4,000 domin kai mai ga masu sayarwa da kanta.

Kafin matatar ta ɗauki wannan matakin ta fuskanci ƙalubale na sayar da manta a Nijeriya inda wasu ‘yan kasuwa suke shigowa da tataccen mai daga ƙetare maimakon saya daga matatar.

Bayan haka ne Matatar Dangote ta tsara wani shirin sayar da mai kai-tsaye ga gidajen mai da kuma yi musu dakon mai a kyauta.

A da Matatar Dangote ta ce shirin zai fara aiki ranar 15 ga watan Agusta, sai dai kuma yanzu ta ce shirin zai fara aiki ne da zarar da yawa daga cikin tankokin dakon sun iso Nijeriya.

Ɗaya daga cikin dalilan da ƙungiyar NUPENG ta bayar na shiga yajin aikin shi ne zargin da suka yi wa Matatar Man Dangote na ɗaukar matakan da ke ƙin jinin ‘yan ƙwadago da kuma yin barazana ga hanyar samun direbobin tankokin dakon mai.

Ƙungiyar ta nuna damuwa kan dagewar da Matatar Mai ta Aliko Dangote ke yi cewa sabbin direbobin tankokin da zai shigo da su ba za su samu damar shiga ƙungiyar ƙwadago ba.

Ƙungiyar ta bayyana wannan matakin a matsayin farmaki kan ‘yancin tarayya wanda kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya tabbatar, da kuma keta dokokin ƙwadago na duniya waɗanda Nijeriya ta amince da su.

“Ba za mu iya tsayawa mu zura ido ba yayin da ake lalata ayyukan mambobinmu,” in ji ƙungiyar.

NUPENG ta ce ta tattauna da ƙungiyar masu motocin haya ta Nijeriya da zummar sauya wa Dangote ra’ayinsa, amma dukkan kiraye-kirayenta ba su yi tasiri ba.

Ƙungiyar ta ce lamarin ya kai maƙura ne a lokacin da kamfanin gidajen mai na MRS, mallakin wani ɗan’uwan Dangote, Sayyu Dantata ya fara ɗaukar direbobin da za su tuƙa tankokin CNG ɗin dakon man Dangote kuma yake tilasta musu sanya hannu kan alƙawarin cewa ba za su shiga ko wace ƙungiya ƙwadago ba, in ji wasu rahotanni.

Tun kafin Matatar Dangote ta fitar da wannan shirin dai, gidan man MRS ya kasance yana sayar da man Matatar Man Dangote a Nijeriya.

Baya ga haka ƙungiyar dillalan mai ta Nijeriya (PETROAN) ta ce tana goyon bayan ƙungiyar ta NUPENG a kan yajin aikinta kuma su ma za su dakatar da sayar da man domin ma’aikatansu ‘yan ƙungiyar ne.

Ita ma ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC) ta goyi bayan wannan yajin aikin inda ta ce ita ma za ta shiga yajin aiki domin mara wa NUPENG baya.

Sai dai kuma gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta kira ƙungiyar ta janye yajin aikinta tare da kiran dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa zuwa teburin sasantawa.

Gwamnatin ta shiga tsakani

Minsitan Ƙwadago na Nijeriya Muhammad Maigari Dingyadi ya kira daukkan ɓangarorin domin tattauna matsalar a wata sanarwar da babban jami’in watsa labaran ma’aikatar ƙwadagon Nijeriya, Patience Onuobia ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ambato ministan yana neman ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya NLC ta janye barazanar shiga yajin aikin.

Tun da fari ya ce: “Na gayyaci dukkan ɓangarorin domin tattaunawar sasanci gobe Litinin, 8 ga watan Satumba, shekarar 2025. Tun da na saka baki, ina roƙon NUPENG ta janye hukuncin da ta yanke na rufe fannin man fetur daga gobe,” in ji ministan.

“Na kuma yi kira ga NLC ta janye gangamin da ta yi wa ƙungiyoyi masu alaƙa da ita cewa su kasance a shirye domin fara yajin aikin goyon bayan NUPENG.

Fannin man fetur ɗin Nijeriya na da muhimmanci ga ƙasar. Ya ƙunshi mafi muhimmancin tattalin arziƙin ƙasar,” a cewar Dingyadi.

Dingyadi ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a warware taƙaddamar cikin lumana kuma ba za a sami katsewar saye da sayarwar mai ba.

Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya tsakanin Matatar Man Dangote da Ƙungiyar Ƙwadagon NUPENG ta masu dakon mai da kuma yadda sakamakon wannan batu zai shafi tattalin arziƙin Nijeriya.