NIJERIYA
3 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya tana yunƙurin kammala tsarin Manufofin Iyali na Ƙasa
Gwamnatin Nijeriya na ƙoƙarin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na Ƙasa wato (National Family Policy) don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar.
Gwamnatin Nijeriya tana yunƙurin kammala tsarin Manufofin Iyali na Ƙasa
Imaan Sulaiman, Ministar Mata ta Nijeriya / Others
8 Satumba 2025

Gwamnatin Nijeriya na ƙoƙarin kammala wani cikakken tsari na Manufofin Iyali na Ƙasa wato (National Family Policy) karkarshin jagorancin Ma’aikatar Mata don karfafa hadin kai, daidaito da adalci a gidaje a fadin kasar.

Da take jawabi a babban taron GS-25 a kan maudu’in ‘Adalci kan fara ne daga gida: Iyali a matsayin ginshiƙin Adalci da Juriya a Al’umma,’ Mataimakiya ta Musamman ga Ministar  a kan Harkokin Mata da Ci gaban Jama'a, Jummai Idonije ta bayyana cewa a yanzu wannan manufar ita ce aka fi bai wa fifiko.

“A karkashin tsarin sabunta fata Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR… Mun karkatar da hankali ma’aikatar zuwa wannan batu, a yanzu haka muna kan shirin kammala manufofin iyali, wannan ya taso ne daga yadda aka kara wa’adin ma’aikatar a yanzu. A da can akwai tsarin amma ba a maganarsa,” in ji ta.

Ta kara da cewa an fadada aikin don kula da mutane masu rauni a fadin kasar: "... kamata ya yi ta zama ma'aikatar harkokin mata da ci gaban zamantakewa, don haka a yanzu muna duba batutuwan mata, yara, iyali da kuma marasa galihu. Don yin duk waɗannan, muna sanya daidaitattun hanyoyin aiki da yawa. "

A kan batun aiwatarwa kuwa cewa ta yi: “…A karkashin Renewed Hope Social Intervention Project 774, aikin zai gudana a kusan duka ƙananan hukumomi 774 a karkashin inuwar Ministar Harkokin Mata, wacce duk wannan ke karkashinta.”

Game da cigaban da ake samu a kan cin zarafin jinsi kuwa, ta ce: "A inda muke, shekaru biyar da suka wuce, ba a nan muke ba a yau. Al'umma tana canzawa, amma ka da mu bar kowa ya ci zarafin 'yan’uwanmu mata ko 'yan’uwanmu maza. Dole ne a adalci ya fara daga iyali."

Gida ne makarantar Farko

A nata jawabin, shugabar tsare-tsare da hulda da jama’a a Guinness Nigeria Chioma Momah, ta ce dole ne iyalai su sanya adalci da juriya a zuƙatan ‘ya’yansu tun daga lokacin haihuwa.

"Gida shi ne makaranta ta farko ta siyasa, mulki da dabi'u. Yayin da muke jiran manufofin gwamnati, dole ne mu yi koyi da adalci da hada kai a gida.

“Idan muka koya wa yara maza da mata juriya, tausayi da jajircewa; za su aiwatar da su a cikin mu’amalarsu da jama'a. Duk wanda muka ga yana yin abin da bai dace ba a matsayin babba, to ya zamo asali ne daga gida."

A halin da ake ciki, Masanin ilimin halayyar ɗan’adam, Oluwatoyin Ogunkanmi, ya bukaci iyaye da su dauki kowane yaro a matsayin na musamman, da dinga yin tattaunawa da su da tabbatar da karfi, da sanya su aiki ta hanyar wanda ya fi iyawa ba ta la’akari da jinsi ba, da samar da tsarin horo, da kuma girmama kowa, tana mai cewa yaran da suka tashi ba tare da samun adalci a gida ba za su nuna son kai a cikin al'umma.