Dakarun sojojin Nijeriya sun ceto mutum 13 da ransu kana sun ciro gawarwaki 27 bayan hatsarin wani jirgin kwale-kwale a ƙaramar hukumar Nguru ta jihar Yobe da ke yakin Arewa maso gabashin Nijeriya.
Wata majiya mai tushe a rundunar sojin kasar ce ta bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Litinin a Abuja.
Majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:15 na safe a ranar Lahadi 4 ga Janairun 2026, lokacin da kwale-kwalen dauke da akalla 'yankasuwa 40 daga kauyen Adiani da ke Jigawa zuwa wata kasuwa a Nguru ya kife a yankin kogin Garbi.
Dakarun rundunar Bataliya ta 241, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da masu nutso na gida sun yi gaggauta isa wurin kana suka yi saurin kai ɗauki, in ji majiyar.
"Aikin haɗin gwiwar binciken da aka gudanar da kuma kokarin ceto mutanen ya kai ga nasarar ceto mutum 13 da rai, yayin da aka ciro gawarwaki 27 daga kogin."
Tuni dai aka binne wadanda suka rasa rayukansu bisa tsari na addinin Musulunci, yayin da hukumomin da abin ya shafa ke daukar karin matakan da suka dace.





















