A cikin ko wace minti 10, abokin zama ko ‘yan’uwa na kashe mace ɗaya a duniya a shekarar 2024, in ji wani rahoton Ofishin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan mata da ƙwayoyi da da laifuka.
Rahoton, wanda aka fitar ranar Talata domin ranar kawar da cin zarafin mata ta duniya , ya bayyana laifin kashe mata a matsayin "tsananin nuna rashin tausayi" na cin zarafin mata da ‘yan mata.
Matan da abokan zaman ko ‘yan uwansu suka kashe su
Rahoton ya nuna cewa kimanin mata da ‘yan mata 50,000 ne abokan zama na ƙut da ƙut da ‘yan’uwa suka kashe a shekarar 2024, ciki har da iyaye maza da iyaye mata da kawunai da ‘yan’uwa maza, lamarin da ya nuna cewa kimanin mata da ‘yan mata 137 ake kashewa a ko wace rana.
"Abokan zama na ƙut da ƙut na yanzu ko kuma na da su suka fi yiwuwar aikata aika-aikar kisan mata, inda suka kai kashi 60 cikin 100 na abokan zama da ‘yan uwa ke kashewa," in ji rahoton.
Binciken ya gano cewa Afirka tana da kaso mafi yawa na kisan da abokan zaman na ƙut da ƙut da ‘yan’uwa ke yi, inda lamarin ya rutsa da kimanin mutum 22,600. A nahiyar Asiya da Turai ne aka fi sami adaddi mafi ƙaranci.
Masu bincike sun jaddada cewa kisan mata wata babbar matsala ce da ke addabar mata a faɗin duniya.
“A bayan kowane adadi, akwai wata mata ko yarinya wadda cin zarafi ko ƙin jinin mata daga maza da kuma al’adu masu lamuntar cin zarafin mata suka katse rayuwarta,” in ji binciken.
Wasu mata sun fi wasu shiga hatsari
Matan da ke cikin siyasa da masu kare haƙƙin ɗa’adam da ‘yan jarida suna yawan fuskantar hare-haren da gangan inda wasunsu ke janyo mutuwa da kuma kisa da gangan, in ji rahoton.
Bincike na Asia-Pacific, ya nuna cewa ɗaya daga cikin kowane mata ‘yan jarida huɗu a duniya kuma ɗaya daga cikin mata uku da ke majalisar dokoki suna samun barzanar kisa ta intanet ko kuma barazanar cin zarafi.
Bincike ya kuma nuna cewa kisan mata yara na faruwa sau biyar cikin matan Kanada fiye da matan da ke cikin ƙasar waɗanda ba ‘yan asalin ƙasar Kanada ba.
Fasahar da ake amfani da ita a kisan mata
Binciken ya nuna cewa uku daga cikin ko wane mata huɗu da aka kashe, wanda ya kashe su ya kasance yana bibiyar su kafin ya kashe su.
"Ana amfani da fasaha domin tabbatar juyi da ƙarfi da kuma sa ido kafin kisan mata," kamar yadda masu bincike suka bayyana, suna masu ƙarawa da cewa ƙarin waɗanda lamarin ya rutsa da su an kashe su ne sakamakon kasancewarsu a kan intanet.
Yawan kisan mata zai iysa zarce hakan
Binciken ya nuna cewa huɗu daga cikin kisan kai 10 da aka yi wa mata da ‘yan mata ba za a iya bayyana su a matsayin kisan kan mata ba domin bambance-bambance na ƙasashe a fannin bincike da rijista na hukunta laifuka.
“Yayin da adadin da aka gabatar a rahoton na da yawa na tayar da hankali, su kaɗan ne daga cikin adadin lamarin,” kamar yadda masu bincike suka bayyana, suna masu bayyana cewa “da yawa sosai” daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su suna tafiya ne ba tare da an ƙirga su ba.
Kisan mata wani sakamako ne na cin zarafin mata da ake maimaitawa wanda za a iya hanawa daga farko.
“Tsare-tsare da suka mayar da hankali kan hanawa daga farko da sauya al’adu da kuma jan hankalin dukkan al’umma domin hana ta lamuntar cin zarafin mata sun fi aiki wajen hana kisa mai alaƙa da jinsi,” kamar yadda masu binciken suka bayyana.
Suna jaddada rawar da ya kamata ‘yan sanda da ɓangaren shari’a ya kamata su taka cikin lamarin.


















