AFIRKA
4 MINTI KARATU
Me bayyana kadarori ke nufi a dokar Nijeriya da kuma tasirin hakan ga dimokradiyya?
Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata ta Nijeriya ta bukaci Bola Tinubu da Kashim Shettima da sauran zababbun gwamnoni da 'yan majalisar dokoki da su bayyana kadarorinsu kafin a rantsar da su
Me bayyana kadarori ke nufi a dokar Nijeriya da kuma tasirin hakan ga dimokradiyya?
Hukumar ta wajabta wa shugaban kasa da gwamnoni da 'yan majalisar tarayya kan su bayyana kadarorinsu kafin a rantsar da su. Hoto/@officialABAT
9 Mayu 2023

Daga Mustapha Kaita

Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata ta Nijeriya CBB ta ce tilas ne zababben shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima su bayyana kadarorin da suka mallaka.

Ta bayyana haka ne kasa da wata guda kafin a rantsar da su. Hukumar ta kara da cewa dole ne zababbun gwamnoni 28 da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai su bayyana kadarorinsu kafin 29 ga watan Mayu.

Jaridar Punch a Nijeriya ta ruwaito Mrs Veronica Kato wadda ita ce mai magana da yawun hukumar tana cewa bayyana kadarori wani sashe ne mai muhimmanci ta bangaren rantsar da shugabanni a dokar kasa.

Ta kuma ce tuni wasu daga cikin zababbun shugabannin suka soma karbar fom din da za su cike bayanai kan kadarorin nasu a ofisoshin hukumar da ke fadin Nijeriya.

Hukumar ta kara da cewa tana bukatar dukkan wanda ya yanki fom din don cikewa ya tabbata ya cike ya mayar ofishin hukumar kafin ranar rantsuwa.

Bayyana kadarori a dokar Nijeriya

Bayyana kadarori a Nijeriya tanadi ne wanda kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya yi inda ya tilasta wa duk wani mai rike da ofishin gwamnati ko dai zababbe ko kuma wanda aka nada ko dauka aiki ko kuma yake aikin kwantiragi ya bayyana kadarorinsa, kamar yadda Hukumar CBB ta bayyana.

A bayanan da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce dole ne wanda zai bayyana kadarorin ya bayyana na matarsa idan ba aikin gwamnati take yi ba, da kuma na iyalansa wadanda suke kasa da shekara 18, sannan ya mayar da fom din da ya cike a cikin kwana 30 bayan karbar fom din.

Dokar hukumar ta tanadi cewa kadarorin da mutum yake da su a lokacin ne kawai zai bayyana, mutum ba zai rubuta kadarorin da yake sa ran mallaka ba.

Haka kuma ta tanadi cewa duka kadarorin da mutum yake da su a wajen Nijeriya dole ne a fayyace su da kuma bayyana darajarsu a kudin kasar da kadarorin suke.

Ta yaya bayyana kadarori ke taimaka wa dimokradiyya?

Nuraddeen Dauda, wanda mai sharhi ne kan lamuran siyasa a Nijeriya, ya bayyana cewa bayyana kadarori na da muhimmanci matuka domin hakan na taimakawa wurin rage cin hanci da rashawa.

Ya ce cin hanci da rashawa na daga cikin abubuwan da suke kawo wa gwamnati tarnaki wurin gudanarwa.

“Idan ana bin wannan doka yadda ya kamata, ana ga wata hanya ce wadda za a rage wannan matsala ta cin hanci da rashawa da ta yi wa Nijeriya dabaibayi.

“Idan mutum ya bayyana kadarorinsa, idan ya sauka kuma za a bibiya a ga nawa ne ya karu a cikin dukiyarsa,” kamar yadda Nuraddeen ya shaida wa TRT Afrika.

Ya kara da cewa wannan hukuma za ta iya bibiya ta ga mutum idan yana da kadarorin da bai bayyana ba, idan ta samu hakan sai ta hukunta shi.

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Hatsarin mota ya yi ajalin fiye da mutum 1,000 a Nijar a shekarar 2023, fiye da 12,000 sun jikkata
Sabbin hotunan tauraron dan'adam sun gano alamun 'kaburburan bai-daya a El-Fasher a Sudan
MDD ta yi gargaɗin cewa yaƙin Sudan na gurgunta tattalin arzikin Sudan ta Kudu
Trump ya ce bai kamata Afirka ta Kudu ta kasance cikin G20 ba, ba zai je taronta a Johannesburg ba
'Yan Sudan sun ba da mummunan labarin yi wa mata fyade yayin da suke tserewa daga Al Fasher
An kashe mutane 40 a harin da aka kai wa taron jana'iza a yankin Kordofan na Sudan: MDD
Yadda biranen Afirka mafiya tsafta suke bayyana sauyin da ake samu a nahiyar
Sojojin Ruwa na Ghana sun kama ‘yan Nijeriya 10 da suka ɓuya a jirgin ruwan Panama a Tema
Harin jirgin sama maras matuƙi na RSF ya kashe mutane da dama a lardin Kordofan na Arewa a Sudan
Fiye da mutum 1,500 sun rasa matsugunansu a Sudan sakamakon taɓarɓarewar tsaro: MDD
Dakarun RSF sun kashe mata 300, sun yi wa 25 fyaɗe cikin awa 48 a Al Fasher – Minista
Amurka ta buƙaci a tattauna domin kawo ƙarshen yaƙin Sudan, ba amfani da ƙarfin soja ba
Ana fargabar dubban mutane na cikin 'mummunan hatsari' a birnin Al Fasher na Sudan da RSF ta ƙwace
Shugabar Tanzania Samia Hassan ta lashe zaɓen ƙasar da kashi 97.66 cikin 100
Tchiroma Bakary: Sojojin Kamaru sun yi wa jagoran 'yan adawar kasar rakiya zuwa wuri mai 'aminci'
Kudirin 1325 ya cika shekara 25: Me ya sa dole Afirka ta jagoranci samar da zaman lafiya a duniya
Dubban mutane sun tsere daga North Kordofan yayin da RSF ta zafafa kai hari a yankin Darfur na Sudan
Fararen-hula 177,000 sun maƙale a Al Fasher na Sudan, yayin da RSF ke ci gaba da kisa - Likitoci
Rundunar RSF ta amsa aikata 'take haƙƙi' a Al Fasher na Sudan
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum 11 'yan yawon bude ido a hatsarin jirgin da aka yi a kasar