Hukumar gudanarwa ta Matatar Man Fetur ta Dangote ta musanta rahotannin da ake yaɗawa waɗanda ke cewa ta sallami ma’aikatanta, inda matatar ta jaddada cewa ta ɗauki matakin sauya fasalin tsarin ma’aikatar ne sakamakon ayyukan zagon-ƙasa.
A wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Jumma’a, ta bayyana cewa ba ta ɗauki wannan matakin bisa son rai ba, inda ta ce ya zama dole ne domin kiyaye ayyukan matatar da kuma tabbatar da tsaro a ciki.
“Matatar Dangote na so ya fayyace rahotannin da suka shafi sake fasalin da ake yi yanzu a cikin matatar. Wannan gyaran ba na son rai ba ne.
“Ya zama dole ne domin kare masana’antar daga yawan ayyukan zagon-ƙasa da suka haddasa damuwa kan tsaro da kuma rage ingancin aiki,” in ji sanarwar.
A cewar kamfanin, sake fasalin da aka yi ya samo asali ne daga nufin kare masana’antar bayan gudanar da ayyukan zagon-ƙasa lokaci bayan lokaci a wasu sassan matatar, wanda hakan ke da mummunan tasiri ga rayuka da kuma tsaro..
“Za mu ci gaba da sa ido sosai kan tsarinmu da kuma wuraren da ke da rauni domin tabbatar da dorewar wannan muhimmiyar kadarar ta ƙasa.
“Yana da matuƙar muhimmanci a kare wannan matata domin amfanin 'yan Nijeriya, abokan hulɗarmu a faɗin Afirka, da kuma dubban mutane da ke dogara da ita domin samun abin rayuwa,” in ji kamfanin.
Masana’antar ta kuma jaddada cewa yawancin ma’aikatanta suna nan suna aiki, inda dubban ‘yan Nijeriya ke ci gaba da aiki a matatar.
“Fiye da ma’aikata 3,000 ’yan Nijeriya suna ci gaba da aiki a matatar mu ta man fetur a halin yanzu.
“Ƙalilan ne kawai daga cikin ma’aikatan da wannan gyara ya shafa, yayin da muke ci gaba da ɗaukar sabbin ma’aikata ’yan Nijeriya ta hanyar shirye-shiryen horaswa na matasa da tsarin ɗaukar ƙwararru,” in ji kamfanin.
Yayin da kamfanin ke sake tabbatar da biyayyarsa ga haƙƙin ma’aikata, ya bayyana cewa yana bin ƙa’idojin ƙasa da ƙasa kan aikin yi, ciki har da damar kowanne ma’aikaci na shiga ƙungiyar ƙwadago ko akasin haka.