An zo zamanin da sai an kunna wa ƙananan yara waƙa a waya sannan suke barci, ba ta hanyar lallashin uwa ba kamar yadda yake a da.
Zamanin da yaro ɗan shekara bakwai ke cin abinci amma waya na riƙe a hannunsa, ba kamar yadda aka saba a baya ba inda iyaye ke hira da su da tabbatar da cewa kowa ya maida hankali kan abinci ya ƙoshi yadda ya kamata.
A yanzu yara ‘yan shekara 10 sun fi mayar da hankali kan koyon abubuwa a bidiyoyi a intanet, maimakon daga dabarun kakanni.
Zamani ya kawo mu lokacin da yara ‘yan matasa suka fi amincewa Ƙirƙirarriyar Basira wajen neman wani sirri maimakon su tattauna da abokai.
Duk inda ka shiga a duniya a yanzu za ka ga yara ba su da aiki sai lallatsa waya, suna kallon abubuwan da yawanci manya ne suka samar amma suke kasa yin iko da su,
Manyan da suka samar da duniyar dijital a yanzu suna fama da wata tambaya marar daɗi: shin sun gaza shawo kai da magance abubuwan da yara ke cin karo da su a intanet ne?
Wannan tambayar ce ta tattara ƙwararru a fannin yaɗa labarai da masana halayyar yara, malamai da masu tsara manufofi zuwa Istanbul don Taron Duniya na Kafofin Watsa Labarai na Yara na TRT wanda ya aka fara a Cibiyar Taron Haliç a ranar 6 ga Disamba, 2025.
Taron na nufin tattauna: yadda yara da iyalai ke mu'amala da kafofin watsa labarai a rayuwarsu a yayin da al’amuran dijital ke bunƙasa.
"Mun gina wannan duniyar ta dijital. Mun shimfiɗa tubalinta. Saboda haka, ba za mu iya zura ido mu bari yaranmu su lalace a cikinta ba," in ji matar Shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdoğan a lokacin bude taron.
Uwargidan ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Hakkin Yara ta Dijital kuma ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki su bi sahu. "Ba za mu iya barin yaranmu su kaɗai a titunan duniyar dijital mara aminci ba,” tana mai cewa cewa dokokin da ake tsara su sun haɗa da sabbin ƙa'idodin kafofin sada zumunta ga yara ‘yan ƙasa da shekaru 15.
Jennifer Kaberi, wacce ta kafa kuma shugabar kamfanin Mtoto News na Kenya mai mayar da hankali kan dijital da kafofin watsa labarai ga yara da matasa, ta jaddada muhimmancin bai wa yara dandali don su yi magana tare da tabbatar da cewa masu yanke shawara suna sauraro.
Ta yi gargadi cewa iyaye na iya kasancewa ko mafi rauni ko mafi ƙarfi a lamarin tsaron dijital.
"Muna kiran kanmu 'yan ciranin dijital, amma mu ne muka ƙirƙiri intanet. ‘Yan ƙarninmu ne na, 'millenials'," in ji Kaberi. "Muna ƙirƙirar wata duniya da ba mu fahimce ta sosai ba, kuma 'ya'yanmu suna tsallen baɗake tare da faɗawa ciki kai-tsaye."
Ana rasa kusanci
Kamar yadda Kaberi ta nuna, fasaha ba kawai tana gasa don jan hankali ba ne a yanzu. Tana gasa da samun kusanci ma.
Yara ƙanana har da waɗanda ba su shirin shiga makarantar firamare ba suna ɓata lokaci mai yawa da maƙalewa wayoyi ko ƙananan komfutoci tsawon sa'o'i ta yadda har ba sa mayar da hankali idan wani ya yi musu magana.
Mu'amala da dijital ta maye gurbin hirarrakin da yara suka saba yi da iyayensu.
Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Turkiyya Burhanettin Duran, wanda kuma ke jagorantar Sashen Harkokin Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasa, ya nuna yadda tasirin dijital ke ƙaruwa a lamarin koyo da hulɗar zamantakewar yara.
"Ba ma son mu raba yara gaba ɗaya da wayoyi ko komfuta, amma dole ne a samar da daidaito mai ma’ana," in ji shi a taron.
Duran ya nuna shirin aiki na ƙasa game da hakkin dijital na yara kuma ya yi gargaɗi cewa abun ciki da tsarin alƙluma wato algorithms ke tsarawa na iya cutar da ci gaban tunani da na ɗabi'a na yara, idan aka bar su sasakai ba a kula ba.
Me ya sa ɗaukar alhaki yake da muhimmanci?
Wata yarinya mai samar da bidiyoyi a intanet, Kayla na daga cikin mahalarta taron, ta yi imanin kowa na da rawar da zai taka wajen tabbatar da cewa nacin maƙalewa duniyar dijital ba ya raba yara daga duniyar ainihi.
"Na ji cewa ya zama wajibi na halarci wannan taron domin in san ta yadda zan iya shiga cikin kafofin watsa labarai fiye don taimakawa yara a fadin duniya," in ji ta.
Darakta Janar na TRT Dr Mehmet Zahid Sobacı ya ce taron ya nuna yadda Turkiyya ke da himma wurin kare yara ta hanyar watsa labarai na gwamnati.
"Muna ganin cewa kare yara ba kawai nauyin ƙasa ba ne amma nauyin duniya ne gaba ɗaya," in ji Sobacı, yana mai cewa TRT na nufin gina "makomar kafofin watsa labarai mai tsabta, mai aminci ga ɗan’adam ga dukkan yara."
Taron ya ƙaddamar da tambayoyi masu mahimmanci: Shin muna kare yara a kan intanet ko kuma sai dai mu yi fatan hakan kawai?
Shin masu samar da bidiyoyi da sauran abubuwa suna la’akari da yara ko kuwa manufarsu ita ce kawai su samu mabiya? Ta yaya iyalai za su yi ƙoƙarin tabbatar da cewa wayoyi da komfuta ba su ɗauke hankulan yara ba.?
Idan yara su ne manyan gobe, kafofin watsa labarai da suke amfani da su a yau za su kayyade duniyar da za su girma a ciki. Siffanta wannan makoma tana farawa a taruka irin na Taron Kafofin Watsa Labarai na Yara a Istanbul.

















