Matar Shugaban Kasar Turkiyya, Emine Erdogan ta sanya hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa domin hana yara a Gaza rasa damarsu ta samun ilimi sakamakon kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a yankin Falasdinawa.
Emine Erdogan ta raka Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan zuwa Taron Kolin Hadin Kan Kasashen Musulmi da Kungiyar Kasashen Larabawa wanda aka gudanar a Doha, babban birnin Qatar, a ranar 15 ga Satumba.
A yayin taron, ta gana da Sheikha Moza bint Nasser, mahaifiyar Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.
Bayan taron, gidauniyar Education Above All Foundation, wacce Nasser ta kafa, ta shirya wata sanarwa ta hadin gwiwa mai taken “Shekara mai tsanani ga ilimin yara da ke rayuwa a yankunan rikici.”
Sanarwar ta yi kira da a dauki matakan gaggawa domin kawo karshen cin zarafin da ake yi wa yara da tsarin ilimi a wuraren da ke fama da rikici, musamman a Gaza.
“Bugu da kari, yayin da ake aiwatar da kisan kiyashi a Gaza, Isra'ila tana kuma amfani da dabarar ‘kisan ilimi’, ta hanyar lalata gaba daya tsarin ilimin Falasdinawa da dakunan karatu da jami’o’i,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa wadannan ayyuka wani bangare ne na dabarar da aka tsara domin lalata da kuma gogewa rayuwar tunani, al’adu da zamantakewar Gaza.
“A yau, mun shiga cikin wannan yunkuri na kawo karshen wannan kisan kiyashi kuma mun yi alkawarin ci gaba da ayyukanmu na samar da damar ilimi da taimaka wa yara su murmure,” in ji sanarwar.
Jakadiyar UNESCO da wasu da dama ciki har da Matar Shugaban Kasar Malaysia, su ma sun sanya hannu kan wannan sanarwar.