Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a ranar Alhamis ya bayyana cewa shirye-shiryen da ake yi na “jefa yankinmu cikin rashin kwanciyar hankali” ba za su yi nasara ba, kuma “masu zubar da jini na mulkin mallaka da aƙidar tsananin son kafa ƙasar Isra’ila” ba za su cim ma burinsu ba.
“Martani mafi ƙarfi ga wannan kisan kare dangi da aka shaida na tsawon watanni 23 da dukkan bil’adama zai fito ne daga Turkiyya da al’ummarta,” in ji Erdogan yayin bikin raba guraben aiki ga dangin shahidai, jarumai, da danginsu a hukumomin gwamnati a Ankara.
“Mun mulki kasashen da ke kalubalantar mu tsawon ɗaruruwan shekaru wadanda su kuma a gomman shekarun baya bayan nan suka samu,” in ji Shugaban Turkiyya, yana mai jaddada cewa, “Mun kasance takobin adalci, muna kawo tsari ga duniya.”
“Mu ba baƙi ba ne ko masu mamaye wannan yanki; mun kasance masu masaukinsa tsawon shekaru dubu kuma za mu ci gaba da kasancewa nan har abada,” Erdogan ya ƙara da cewa.
Erdogan ya mayar da martani ga Netanyahu
Maganganun Erdogan na baya-bayan nan sun kasance martani ga rikicin kalamai tsakaninsa da Netanyahu, wanda ya fara ne lokacin da shugaban Isra’ila ya ambaci sunan Erdogan yayin wani biki a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, tare da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da Jakadan Mike Huckabee a ranar Litinin.
A yayin bikin, Netanyahu ya bayyana cewa, “Wannan birnin namu ne. Erdogan, ba naka ba ne. Birnin Ƙudus namu ne har abada, kuma ba za a sake raba shi ba,” yana mai jaddada cewa ba za a taba kafa wata ƙasa ta Falasɗinu ba.
Netanyahu ya kuma nuna wani allo mai rubutun Ibiraniyanci da aka gano kusa da Titin Pilgrimage a Birnin David a lokacin Daular Usmaniyya, yana tuna yadda gwamnatocin Turkiyya suka ƙi mika shi tun lokacin da Isra’ila ta fara neman sa a shekarar 1998.
Netanyahu ya ce tsohon takwaransa, Mesut Yilmaz, ya ƙi amincewa da bukatarsa saboda tsoron cewa masu zabe karkashin jagorancin tsohon magajin garin Istanbul, Erdogan, za su fusata idan aka bai wa Isra’ila wannan allo.
Shugaban Isra’ila ya yi ikirarin cewa ƙin amincewar Ankara ya samo asali ne daga damuwa cewa kayan tarihi zai tabbatar da cewa Birnin Ƙudus birni ne na Yahudawa shekaru 2,700 da suka gabata.
A washe garin ranar ne Erdogan ya sake jaddada matsayinsa da cewa, “Netanyahu bai kamata ya manta da matsayina shekaru 27 da suka gabata ba,” yana mai alkawarin cewa Turkiyya “ba za ta bari hannun da ba a yarda da shi ya ɓata Birnin Ƙudus ba.”
“Na san cewa zafin zuciyar waɗannan mutane masu tunanin Hitler ba zai taɓa gushewa ba,” in ji shi. “Bari su ci gaba da nuna fushi. Mu, a matsayin Musulmai, ba za mu ja da baya daga hakkokinmu kan Gabashin Birnin Ƙudus ba.”