Daraktan Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran ya ce "duniya na fama da matsalar Isra'ila", yana mai bayyana ta a matsayin gwamnati mai ɓarna da ke keta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ciyar da kanta da rikici maimakon tsarin doka.’’
Kalaman Duran sun zo ne a ranar Laraba yayin taron "Gaza: Humanity’s Litmus Test", wanda aka gudanar a Hukumar Sadarwar Turkiyya da ke Ankara inda jami'an diflomasiyya, da malamai da kuma 'yan jarida suka gabatar da jawabai.
A jawabin da ya gabatar na musamman, Duran ya jaddada matsayin Turkiyya ƙarkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan na: tabbatar da samar da hanyoyin tsagaita wuta na dindindin, tare da tabbatar cewa an isar da kayayyakin jinƙai, da kuma kafa ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta.
Ya jaddada cewa "al'ummar duniya ba za su iya yin watsi da gaskiyar abin da Isra'ila ke yi ba, wanda ke barazana ga zaman lafiyar yanki da ma duniya baki daya."

Sanya batun Gaza a kan gaba a duniya
Duran ya jaddada rawar da hukumar sadarwa ta Turkiya ke takawa wajen tallafa wa Falasɗinu a "ɓangaren sadarwa."
Ta hanyar amfani dabarun diflomasiyya da kayan aikin yada labarai na zamani, a cewar Daraktan "gaskiyar yanayin da Gaza ke ciki zai kasance a kan a ajandar duniya."
Ya yi ƙarin haske game da koƙarin da aka yi wajen fallasa sama da ƙarairayi 250 na Isra'ila, wanda ya kai ga sadaukarwar mujalloli da manyan tarukan ƙasa da ƙasa, da na baje-koli da kuma tura ‘yan jarida wurare don ɗaukar sahihan labarai.
"Sadarwa a gare mu ba kawai hanyoyin samun ilimi ba ne, batu ne na lamiri," in ji Duran. "Muna ƙoƙarin fakar da duniya tare da tabbatar da cewa an adana tarihin munanan ayyukan da Isra'ila ta aikata."
Kafofin sadarwa a kan gaba
Duran ya yi jinjina ta musamman ga kafafen yada labaran Turkiyya, inda TRT da Kamfanin Dillancin Labarai na Anadolu suka yi fice wajen yada labaransu.
Duk da irin tashin hankali da tsaiko da suke fuskanta, 'yan jaridar Turkiyya "ba su taba yin watsi da matsayinsu na zama muryar Gaza ba."
TRT Haber ta gabatar da rahotanni sama da 20,000 daga Gaza, kuma TRT World ta sadaukar da rabin lokacinta ga Falasdinu da Gaza, in ji shi.
Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya yada labarai kusan 144,000 a cikin harsuna 13, tare da hotuna 200,000 da bidiyo 15,000, wadanda da yawa daga cikinsu a yanzu sun zama shaida a shari'ar duniya.
Tashar dijital ta Turkiyya Tabii ta kaddamar da wani sashe mai suna "Labarun Falasdinawa", wanda ke karyata labaran da ake yada kai-tsaye a duniya.
Hukumar Sadarwar ta kuma kammala wani littafi da ke tattara bayanan 'yan jaridun da aka kashe a Gaza, inda ta bayyana cewa Isra'ila ta kai hari da gangan kan ma'aikatan jaridu kusan 300 wadanda kawai manufarsu ita ce "ba da rahoton gaskiya."
“Tafiyar lamiri”
Duran ya soki yadda Ƙasashen Yamma ke ‘‘nuna fuska biyu" a harkokin yada labaransu, yana zargin kafofin da nuna son kai da kuma yada labaran karya.
Sabanin haka, ya kwatanta kafofin yada labarai da cibiyoyin sadarwa na Turkiyya a matsayin jagorar "tafiyar lamiri" na duniya.
"Sojojin Isra'ila na iya tarwatsa kyamarorin 'yan jaridunmu, amma ba za su iya hana bayyana gaskiya ba," in ji Duran, yayin da yake ambato Shugaban Ƙasar Turkiyya.