Mutanen Kenya na alhinin rasuwar wani toron giwa mai farin jini da ya yi suna saboda girman haurensa, wanda tsawon ransa a daji, inda har ya zamo wata alamar nasarar ƙoƙarin ƙasar na kare dabbobi daga masu farauce su.
Namijin giwar wanda ya rasu a ranar Asabar, ana kiransa da Craig. Ya rayu a Gandun Dajin Amboseli, wani wurin da aka killace a kudanci Kenya, wanda masu yawon buɗe-ido ke so, in ji sanarwar Hukumar Kula da Dabbobin Daji ta Kenya.
“Craig, shahararren toro ne mai dogon haure wanda haƙoransa ke gogar ƙasa idan yana tafiya cikin ƙasaita, wanda ya rasu yana da shekaru 54,” in ji sanarwar.
Hukumar Amboseli Trust for Elephants ta ce Craig ya rasu ne saboda dalilan ɗabi'a. Ƙungiyar mai kare muhalli ta bayyana godiya ga kowa da ya yi aiki don taimaka wa dabbar ta “rayu har ta mutu cikin yanayi na ɗabi'a”.
Tashar gidan talabijin ta gida NTV ta nuna wani shiri kan rasuwar Craig, inda ta bayyana giwan a matsayin dabba mai wuyar samu, kuma ɗaya cikin ragowar giwaye da aka tabbatar suna rukunin masu girman haure a Afirka'.
Rukunin giwayen na nufin giwa namiji mai haƙori da kowannensu yana da nauyin fiye da kilogram 45. Haure mai irin wannan girman yana da matuƙar tsayi, har yana gogar ƙasa yayin da giwa ke tafiya, a cewar Tsavo Trust, wata ƙungiya mara neman riba a Kenya.
A Gandun Dajin Amboseli, akwai wani wuri da yake da tsirrai mai yanayin savanna da filayen ciyayi kusa da ke kusa da iyakar Tanzania. Craig ya zama mai jan hankalin masu yawon buɗe-ido.
An bayyana Craig a matsayin mai natsuwa, “sau da yawa yana dakatawa cikin haƙuri yayin da baƙi ke ɗaukar hotunansa da bidiyo,” in ji Hukumar Kula da Dabbobin Daji.
Gandun dajin da wuraren killace dabbobi na Kenya, suna adana nau'o'in dabbobi daban-daban, kuma suna jawo hankalin miliyoyin baƙi a kowace shekara, wanda hakan ya sa ƙasar ta zama babban wuri na yawon shaƙatawa.
Yawan giwaye a wajen ya ƙaru daga 36,280 a 2021 zuwa 42,072 a 2025, in ji sabbin bayanan hukuma.
A Ma'ajiyar Ƙasa ta Mwea, wani wuri a gabashin Nairobi, babban birnin Kenya, yawan giwaye ya ƙaru sosai, har ya yi wa tsarin muhalli yawa, wanda ya sa aka buƙaci sauya mazaunin kusan giwaye 100 a 2024.
Jinsin giwar savanna ta Afirka, ita ce mafi girma a dabbobin tsandauri. Toron giwar na iya kaiwa nauyin kimanin tan 6. Craig ya haifi giwaye da dama, wanda ya tabbatar da cewa zuriyarsa mai ƙarfi za ta ci gaba a cikin ƙarnuka masu zuwa,” in ji hukumar kula da dabbobi.















