Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da yunƙurin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, musamman Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), domin ɓata masa suna.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya nuna damuwarsa kan sabbin abubuwan da suka faru a dangantakarsa da gwamnan, wanda a baya ya taɓa yi masa aiki a matsayin mataimaki na musamman, babban sakataren ofishinsa da kuma kwamishina.
Ya ce dangantakarsu ta shafe shekaru 43 bisa amana, yana mai cewa Yusuf ne kuma ɗan takarar da tafiyarsu ta siyasa ta zaɓa a zaɓukan gwamnan Kano na 2019 da 2023, inda ya samu nasara a zaɓen 2023.
Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnan ya taɓa miƙa takardar buƙata ga EFCC domin ta gudanar da bincike a kansa, amma bayan ya gaza shawo kan hukumar, sai ya koma ga wata ƙungiya.
“Muna da yakinin cewa a watannin baya da kansa gwamna [Abba Kabir] ya kai goron gayyata ga EFCC don su yi farautatata,” in ji shi.
Ya kuma zargi gwamnan da amfani da ƙungiyar Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative (SACGGI) wajen shirya zanga-zanga a hedikwatar EFCC, da nufin matsa wa hukumar lamba.
Kwankwaso ya kuma yi zargin cewa waɗannan matakai na da alaƙa da siyasa, kuma an ɗauke su ne domin daƙile tafiyarsu gabanin babban zaɓen 2027.
Kwankwaso ya kuma yi zargin cewa waɗannan matakai na da alaƙa da siyasa, kuma an ɗauke su ne domin raunana tafiyarsu gabanin babban zaɓen 2027.
Haka kuma ya yi zargin cewa ɓata suna bai tsaya a kansa kaɗai ba, har ma ya shafi ɗan takarar gwamnan Kano na NNPP, Kwamared Aminu Abdussalam, wanda a halin yanzu ke kare cancantarsa a gaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kuma kotuna.
Sai dai tsohon gwamnan ya yaba wa EFCC kan yadda ta gudanar da gayyatar da ta taɓa yi masa a baya, yana mai cewa ya kiyaye mutuncinsa a tsawon shekarun da ya yi yana hidimar jama’a.
Ya buƙaci ’yan siyasa da su mutunta ’yancin hukumomin gwamnati, tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya rage amincewar jama’a da waɗannan hukumomi.















