| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya da UAE sun soke harajin kayayyaki 13,000 da suke cinikayya a kansu
Kasashen biyu sun dauki wannan matakin ne bayan sun cim ma wata yarjejeniyar bunkasa kasuwanci tsakaninsu.
Nijeriya da UAE sun soke harajin kayayyaki 13,000 da suke cinikayya a kansu
Shugaba Tinubu da Sarki Mohamed bin Zayed Al Nahyan sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama / Nigerian Government
14 Janairu 2026

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa kasar ta soke harajin da take karba a kan kayayyaki 6,243 da ake shigowa da su daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) yayin da ita ma UAE ta soke harajin kayayyaki 7,315 da ake kai wa kasar daga Nijeriya.

Kasashen biyu sun dauki wannan matakin ne bayan sun cim ma wata yarjejeniyar bunkasa kasuwanci tsakaninsu.

Ma’aikatar masana’antu da kasuwanci da zuba jari ce ta bayyana haka  a ranar Talata bayan kasashen biyu sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da aka yi wa lakabi da Nigeria–UAE Comprehensive Economic Partnership Agreement signed in January 2026.

Kamar yadda ma’aikatar ta bayyana yarjejeniyar za ta bunkasa harkokin kasuwanci da samar da wasu sabbin damarmaki cinikayya da sabbin hanyoyin zuba jari a UAE da Nijeriya. Kuma wannan wani mataki ne na kokarin karkatar da akalar tattalin arzikin Nijeriya daga rage dogaro kan harkar mai.

Masu AlakaTRT Afrika - Nijeriya da UAE sun shirya tattaunawa kan batutuwan da suka shafi biza

A karkashin wannan sabuwar yarjejeniya, Nijeriya ta soke haraje-haraje a kan kayayyaki 3,949 wanda hakan ya kai kaso 63.3 cikin 100 na duka kayayyakin.

Yayin da dama can Nijeriya ta soke haraji a kan kayayyaki 2,294 tsawon shekaru biyar, yanzu Nijeriya kayayyaki 123 ne kawai ba ta soke harajinsu ba.

A nata bangaren UAE ta soke haraji a kan kayayyaki 2,805 wanda hakan ya kai kaso 38.3 cikin 100 na jimmalar kayayyakin kuma nan da shekaru uku za ta cire haraji a kan kayayyaki 1,468.

Sannan za ta cire haraji a kan kayayyaki 3,042 a cikin shekaru biyar masu zuwa.Kasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata bayan Ministar Masana’antu da Kasuwanci da Zuba Jari Jumoke Oduwole da taimakon Ministan Shari’a da kuma hukumar kwastam.

Minista Jumoke da Ministan Kasuwanci da Kasashen Ketare na UAE Dr Dr Thani bin Ahmed Al Zeyoudi sun sanya hannnu kan yarjejeniyar ne a gaban Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da kuma Shugaban UAE Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan.