Yayin da shekarar 2025 ke ƙarewa a Larabar nan, wani mai goyon bayan Manchester United zai ƙare shekara ba tare da aske gashin kansa ba ko sau guda, inda ya cika kwanaki 452 cur.
Mutumin mai suna Frank Ilett ya sha alwashin ba zai aske gashin kansa ba, har sai ƙungiyar ta ci wasanni biyar a jere ba yankewa.
Ilett wanda ke da laƙabin “The United Strand” a shafukansa na soshiyal midiya ya ɗauki wannan alƙawari ne a Oktoban 2024, bayan an naɗa Ruben Amorim ya zama sabon kocin United.
Ko a halin yanzu ma, tuni gashinsa ya cika kai kamar salon da ake cewa “afro”, ga shi United ba ta ɗauki hanyar jeranta lashe wasanni biyar ba. Ga muhimman abubuwa biyar game da Frank Ilett:
1- Dan asalin Oxford ne
Frank Ilett yana da shekaru 29 a duniya kuma mai ƙirƙira da wallafe-wallafe ne a shafukan sada zumnuta. Ya yi suna ne tun sanda ya ɗauki alƙawari a Oktoban 2024, cewa ba zai sake aski ba sai United ta ci wasa biyar a jere.
Da zarar burinsa ya ciki, ya ce zai aske gashinsa a filin wasa na Old Trafford, sannan ya sadaukar da kuɗin da ya tara ga cibiyar Little Princess Trust, mai ba da agajin gashin ɗaurawa ga yaran da cutar kyansa ta kwashe wa gashin kai.
Ilett ɗan asalin birnin Oxford na Ingila ne, amma a yanzu yana zaune a ƙasar Sifaniya. Ana kallon alwashinsa a matsayin wani abu da yake da niyyar taimaka wa United farfaɗo da tagomashinta.
2- Tarin mabiya a soshiyal midiya
Frank Ilett ya saka wa kansa laƙabin “The United Strand”, kuma yana yi wa kansa kirarin shi ne asalin wanda ya fara ta’adar tara gashi don nuna soyayya ga Manchester United.
Waannan ya sa ya samu tarin mabiya a shafuka sada zumunta, inda zuwa yanzu yake da jimillar mabiya sama da miliyan ɗaya da rabi, inda a Facebook yake da dubu 47.
Ya faɗa a shafinsa na Facebook cewa yana da mabiya dubu 772 a Instagram, da dubu 576 a TikTok, da dubu a 155 a TikTok na biyu, da dubu 79 a YouTube, da dubu 18 a X.
3- United ta hukunta wanda ya taɓa shi
A watan Oktoba, hukumomin United sun hukunta wani da ya hari Frank Ilett, da haramcin shiga filin wasanta na Old Trafford. Wato dai alamu sun nuna cewa akwai wasu magoya bayan United da Ilett bai burge wa.
Lamarin ya faru ne a Satumba, bayan wani wasa da United ta doke Chelsea da ci 2-1, inda wani cikin ‘yankallo ya ja gashin Ilett, kuma aka yi ta yaɗa bidiyon abin da ya faru.
4- Neman Beckham ya masa aski
Wani tsohon ɗanwasan Manchester United, Nani ya nemi tauraron tsohon ɗanwasan United, David Beckham ya yi wa Ilett aski da zarar ƙungiyar ta cika wasanni biyar tana yin nasara a jere.
An ambato Nani na cewa “Ina tunanin wani gwarzo cikin tsaffin ‘yanwasan United ne ya kamata ya ya masa aski," don taya shi murnar cika wannan alƙawarin nasa.
5- Yiwuwar yin kitso
Wani tsohon ɗanwasan Man U, Wes Brown ya gargaɗi Ilett cewa akwai yiwuwar nan gaba sai ya yi kitso irin na ‘yan Afirka, bayan wani wasa da Nottingham Forest ta farke wasa aka tashi yi canjaras da United 2-2.
Kafin wasan na 1 ga Nuwamba, United ta buga wasa uku tana yin nasara a jere. Wannan ne ya sa Brown wanda ya taɓa buga wa United a matsayin ɗanwasan baya yake tararrabi kan makomar gashin Ilett.












