Rahotanni daga Sifaniya na cewa Lionel Messi na fuskantar barazanar rushe masa wani katafaren gida da ke ƙasaitaccen tsibirin Ibiza na Sifaniya.
Ƙimar katafaren gidan na shaƙatawa tkai dala miliyan $12, kuma yana yankin Sant Josep de Sa Talaia a gaɓar yammacin tsibirin Ibiza.
An gina gidan a wani fili mai faɗin murabba’in mita 16,000 a filin da doka ta hana yin gini a wajen, kuma ba tare da an samu izini yin ginin ba.
A 2022 ne Messi ya sayi gidan daga hamshaƙin ɗan kasuwa ɗan ƙasar Switzerland, Philippe Amon, amma an gano ginin gidan ya saɓa wa dokar tsara birane.
A baya bayan nan batun gidan ya ƙara zama abin ce-ce-ku-ce, musamman lokacin da ƙungiyar fafutukar kare yanayi, Futuro Vegetal ta lalata gidan a bara.
Agustan 2024
Sakamakon taƙaddama da ake ci gaba da yi a kan gidan na ɗan wasan ɗan asalin Argentina, akwai haɗarin rushe wani ɓangarensa matuƙar ba a warware taƙaddamar ba.
A wajen masana harkokin gidaje, wannan katafaren gida yana cikin rukunin “kadara mai guba”, wadda ba ta sayuwa balle ba da haya.
Bugu da ƙari, dokar magajin gari ta haramta wa Messi yin wani aiki kan gidan, wanda yake da tafkin ninƙaya mai faɗin murabba’in mita 92 da filin ƙwallon ƙafa na musamman.
A Agustan 2024, Ƙungiyar Futuro Vegetal ta masu kare yanayi ta kai farmaki kan katafaren gidan, inda ta ɓata shi da ja da baƙin fenti, kuma ta yaɗa hotunan abin da ta yi a kafofin sada zumunta.
Akwai rahotannin da ke cewa Lionel Messi ya kai ƙarar ƙungiyar kan laifin lahanta gidan, yana neman diyyar fam 50,000.