| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
‘Yansandan Nijeriya sun gayyaci Fasto Chris Okafor bisa zarge-zargen aikata fyaɗe
Ɗaya daga cikin zarge-zargen da suka fi ɗaukar hankali shi ne na jarumar Nollywood Doris Ogala, wacce, a cikin jerin bidiyoyin Instagram da ta wallafa a ranar 14 ga Disamba, ta yi ikirarin cewa ta yi alaƙa ta jima'i da fasto ɗin.
‘Yansandan Nijeriya sun gayyaci Fasto Chris Okafor bisa zarge-zargen aikata fyaɗe
Ana zargin pastor din da laifukan aikata fyade da cin zarafin mambobin cocin da ma cin amanar jama'a. / Nigeria Police
5 Janairu 2026

Rundunar ‘yansanda a jihar Legas da ke kudu maso-yammacin Nijeriya ta gayyaci babban fasto na rukunin cocin ‘Mountain of Libertation and Miracles Ministries’ Fasto Chris Okafor bisa zarge-zargen aikata fyaɗe a lokuta daban-daban.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi da daddare, Jami'ar Hulɗa da Jama'a ta 'Yansandan Legas, Abimbola Adebisi, ta ce an umarci malamin cocin ya gabatar da kansa ga Sashen Binciken Laifuka na Jiha (SCID), Panti, ranar Litinin, da ƙafin karfe 10:00 na safe, domin amsa tambayoyi game da zarge-zargen.

A cewar sanarwar, Kwamishinan 'Yansanda na Jihar Legas, Olohundare Jimoh, ya umarci Mataimakin Kwamishinan 'Yansanda mai kula da SCID da ya gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen laifuka da dama da ake yi wa Fasto Okafor.

'Yansandan sun bayyana cewa an bai wa faston takardar gayyata ta hannun lauyansa kuma ana sa ran zai bayar da haɗin kai ga masu bincike yayin da ake ci gaba da binciken manyan laifuka da ake zargin sa da aikatawa.

Jimoh ya kuma bayar da umarni a samar da tsaro nan-take ga mutanen da aka ci zarafi don su je su bayar da bayani a gaban SCID, Panti, inda tuni aka riga aka fara bincike.

Rundunar ta tabbatar wa jama'a cewa za a tsare sirrin duk wanda abin ya shafa da shaidu kuma a kare su yadda ya kamata.

Masu AlakaTRT Afrika - Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta kama waɗanda ake zargi da fille kan almajiri a Adamawa

An yi kira ga mutanen da suka faɗa cikin wannan lamari, da kuma mutanen da ke da bayanai masu inganci ko shaidu masu alaƙa da binciken, da su kai rahoton hakan ga SCID kai-tsaye ko ta hanyar Sashen Hulɗa da Jama'a na 'Yansanda a Rundunar 'Yansandan Jihar Legas.

Kwamishinan 'Yansanda ya nanata jajircewar Rundunar wajen tabbatar da ƙwarewa, gaskiya, da kuma rashin nuna son kai wajen gudanar da binciken, yana mai jaddada cewa babu wani mutum da ya fi ƙarfin doka.

"An bai wa fasto ɗin takardar gayyata ta hannun wakilinsa na shari'a kuma ana sa ran zai bayar da cikakken goyon baya ga Sashen Binciken Laifuka, Panti, a ci gaba da binciken zargin manyan laifuka da sauran cin zarafi da ake yi masa," in ji sanarwar.

Gayyatar da binciken sun zo ne a daidai lokacin da wasu zarge-zargen suka bayyana a shafukan sada zumunta kan Okafor a watan Disamban 2025.

Ɗaya daga cikin zarge-zargen da suka fi ɗaukar hankali shi ne na jarumar Nollywood Doris Ogala, wacce, a cikin jerin bidiyoyin Instagram da ta wallafa a ranar 14 ga Disamba, ta yi ikirarin cewa ta yi alaƙa ta jima'i da fasto ɗin.

Ta yi zargin cewa dangantakar ta fara ne a shekarar 2017 kuma ta shafe shekaru tara, tana zarginsa da karya alƙawarin aure, yaɗa hotuna da bidiyoyin tsiraicinta, da kuma taimaka wa wajen wargaza aurenta na baya.

Rumbun Labarai
Fiye da mutum 50 ne suka mutu a harin 'yan bindiga a jihar Neja ta tsakiyar Nijeriya
Nijeriya ta kama Indiyawa 22 bisa zargin shigar da hodar ibilis ƙasar
Aƙalla mutane 25 sun mutu, an ceto 13 a hatsarin kwale-kwale a Jihar Yobe ta Nijeriya
An kashe fiye da mutum 30, an sace wasu da dama a Jihar Niger a tsakiyar Nijeriya: 'yansanda
Sojojin Nijeirya sun gano albarusai masu yawa a cikin kwata a Maiduguri
Sakon Shugaba Tinubu na Sabuwar Shekara: Za a tallafa wa mutum 1,000 a kowace mazaɓa a Nijeriya
Abin da bincike ya gano na musabbabin annobar cutar ƙoda a Jihar Yobe
Rundunar sojin Nijeriya ta kashe ‘yan ta’adda 47 a farmaki da ta kai a faɗin ƙasar
Gobara ta ƙona Masallacin Shitta-Bey da ke Lagos wanda ke da alaƙa da Daular Usmaniyya ta Turkiyya
Kotu ta ba da umarnin tsare Abubakar Malami da ɗansa a gidan yarin Kuje
Wani abu ya fashe a Babban Asibiti a Jihar Kebbi ta Nijeriya
‘Yan jarida bakwai sun mutu sakamakon hatsarin mota a Gombe
Siyasar Kano: Shin Kwankwaso ne zai tura Gwamna Abba  Jam'iyyar APC ko kuwa gaban kansa yake son yi?
Shugaba Tinubu ya tafi Turai don ci gaba da hutun ƙarshen shekara
Bam da aka binne a titi ya halaka mutane a Jihar Zamfara, wasu da dama sun jikkata
Mun tuntuɓi Turkiyya domin neman agaji kan matsalar tsaro – Shugaban Nijeriya Tinubu
Hare-haren Amurka sun sauka a wuraren da babu 'yan ƙungiyar Daesh a Sokoto, in ji mazauna yankin
Jirgin Saman Sojin Nijeriya C-130 da aka tsare a Burkina Faso ya isa Portugal domin yin gyara
Da haɗin gwiwarmu Amurka ta kai hari Nijeriya: Ma'aikatar Harkokin Waje
Amurka ta kai hari kan mayaƙan Daesh a Nijeriya, in ji Donald Trump