Tawagar ‘yan wasan Maroko ta ‘yan ƙasa da shekara 20 ta ci kofin duniya a karon farko ranar Lahadi bayan ta doke takwararta ta Argentina wadda ta fi kowace ƙasa cin kofin a tarihi da ci 2-0 a wasan ƙarshen da aka yi a Chile.
Yassir Zabiri ya saka tawagar Atlas Cubs kan gaba minti 12 da fara wasa da bugun tazara kuma ya zura ƙwallo na biyu a raga a minti 29 da fara wasa a wani ƙwallon da ya buga da ƙarfi.
Argentina ta yi ƙoƙarin kutsawa, amma jajircewar tsaron gidan Maroko da kuma wani ƙwallon da gola Ibrahim Gomin ya ture a minti 83 da fara wasa sun hana yunƙurin ƙasar kai ga ci.
Tawagar ta Maroko, wadda koci Mohamed Ouahbi ke horaswa, ta kasance a tsuke garam kuma ta kasance mai juya akalar wasan inda ta yi nasara mai cike da tarihi.
Maroko ta kai ga wasan ƙarshe ne bayan ta doke Sifaniya da Brazil da Korea ta Kudu da Amurka da kuma Faransa. Nasararar ta zamto wani ƙari a wata shekarar da Maroko take samun tagomashi a fagen tamaula.