| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Trump ya ƙara Nijeriya da ƙasashen Afirka 12 a jerin waɗanda za su biya $15,000 na bizar Amurka
Gwamnatin Amurka ta ninka yawan ƙasashen da ta sanya wa 'yan ƙasarsu dole su biya kuɗin aijiya ya kai har $15,000 na samun bizar shiga kasar
Trump ya ƙara Nijeriya da ƙasashen Afirka 12 a jerin waɗanda za su biya $15,000 na bizar Amurka
‘Yan ƙasashen da aka kara za su fara biyan kuɗin ne daga ranar 21 ga Janairun 2026 / Reuters
7 Janairu 2026

Gwamnatin Trump ta kusa ninka adadin ƙasashen da masu riƙe da fasfo ɗinsu za su ba da kuɗin aijiya na karya ka’idar bizar zama a Amurka wanda ya kai har $15,000.

Matakin hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan ƙara ƙasashe bakwai cikin jerin ƙasashen da aka ware da za su ba da kuɗin aijiyar da jimillarsu ya kai 13, a yanzu ma'aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta ƙara wasu 25 a ranar Talata.

‘Yan ƙasashen da aka kara za su fara biyan kuɗin ne daga ranar 21 ga Janairun 2026, a cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na travel.state.gov.

Wannan mataki dai na nufin cewa ƙasashe 38, waɗanda mafi yawa daga cikinsu ƙasashen Afirka ne da wasu daga yankin Latin Amurka da Asiya a yanzu suna cikin jerin, wanda hakan ya sa tsarin samun bizar shiga Amurka ba zai matukar tsada ga mutane da dama.

Masu AlakaTRT Afrika - Gwamnatin Nijeriya ta koka game da sabuwar dokar tafiye-tafiye da Amurka ta fitar

ƙarin ƙasashen da wannan doka ta biyan kuɗin aijiyar ƙarya ka’idar bizar Amurka ta shafa sun hada da Algeria da Angola da Antigua da Barbuda da Bangladesh da Benin da Burundi da Cabo Verde da Cuba da Djibouti da Dominica da Fiji da Gabon da Côte d'Ivoire, Kyrgyzstan da Nepal da Nijeriya da Senegal da Tajikistan da Togo da Tonga da Tuvalu da Uganda da Vanuatu da Venezuela da kuma Zimbabwe.

A yanzu sun hada da ƙasashen Bhutan da Botswana da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Gambia da Guinea da kuma Guinea-Bissau da Malawi da Mauritania da Namibia da Sao Tome da Principe da Tanzania da Turkmenistan da kuma Zambia a cikin jerin gaba ɗaya.

Waɗannan sharuɗɗa na daga cikin ƙoƙari da gwamnatin Trump ke yi na ƙara tsaurara buƙatun shiga Amurka, gami da tilasta wa 'yan ƙasashen da ke buƙatar bizar Amurka su amsa tambayoyi ciki har da buƙatar bayyana tarihin shekaru na da abubuwan da suke wallafa wa a kafofin sada zumuntarsu na zamani da kuma bayanai game da tafiye-tafiye da zaman su da iyalansu a baya.

Jami'an Amurka sun kare sharuɗɗan na ajiyar kuɗin wanda zai iya kaiwa daga $5,000 har zuwa $15,000, inda suka bayyana cewa suna da tasiri wajen tabbatar da cewa 'yan ƙasashen da ke da niyya shiga Amurka ba su wuce lokacin ka’idar zama da aka ba su na biza ba.

Ba da kuɗin aijiyar ba wai yana nufin tabbas mutum zai samu bizar shiga kasar ba ne, za a mayar da adadin ƙudin idan aka hana mutum bizar ko kuma idan wanda aka bizar ya cika sharuddan da ake buƙata na biza.

Rumbun Labarai
Sojojin Nijeriya sun ciro gawarwaki 27 a hatsarin kwale-kwale a Jihar Yobe
Fiye da mutum 50 ne suka mutu a harin 'yan bindiga a jihar Neja ta tsakiyar Nijeriya
‘Yansandan Nijeriya sun gayyaci Fasto Chris Okafor bisa zarge-zargen aikata fyaɗe
Nijeriya ta kama Indiyawa 22 bisa zargin shigar da hodar ibilis ƙasar
Aƙalla mutane 25 sun mutu, an ceto 13 a hatsarin kwale-kwale a Jihar Yobe ta Nijeriya
An kashe fiye da mutum 30, an sace wasu da dama a Jihar Niger a tsakiyar Nijeriya: 'yansanda
Sojojin Nijeirya sun gano albarusai masu yawa a cikin kwata a Maiduguri
Sakon Shugaba Tinubu na Sabuwar Shekara: Za a tallafa wa mutum 1,000 a kowace mazaɓa a Nijeriya
Abin da bincike ya gano na musabbabin annobar cutar ƙoda a Jihar Yobe
Rundunar sojin Nijeriya ta kashe ‘yan ta’adda 47 a farmaki da ta kai a faɗin ƙasar
Gobara ta ƙona Masallacin Shitta-Bey da ke Lagos wanda ke da alaƙa da Daular Usmaniyya ta Turkiyya
Kotu ta ba da umarnin tsare Abubakar Malami da ɗansa a gidan yarin Kuje
Wani abu ya fashe a Babban Asibiti a Jihar Kebbi ta Nijeriya
‘Yan jarida bakwai sun mutu sakamakon hatsarin mota a Gombe
Siyasar Kano: Shin Kwankwaso ne zai tura Gwamna Abba  Jam'iyyar APC ko kuwa gaban kansa yake son yi?
Shugaba Tinubu ya tafi Turai don ci gaba da hutun ƙarshen shekara
Bam da aka binne a titi ya halaka mutane a Jihar Zamfara, wasu da dama sun jikkata
Mun tuntuɓi Turkiyya domin neman agaji kan matsalar tsaro – Shugaban Nijeriya Tinubu
Hare-haren Amurka sun sauka a wuraren da babu 'yan ƙungiyar Daesh a Sokoto, in ji mazauna yankin
Jirgin Saman Sojin Nijeriya C-130 da aka tsare a Burkina Faso ya isa Portugal domin yin gyara