| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Nijeriya ta yi watsi da amincewar da Isra’ila ta yi wa Somaliland a matsayin 'yantacciyar ƙasa
Nijeriya ta fitar da wata sanarwa ta daban da ke yin Allah wadai da matakin na Isra'ila. Ta kuma sanya hannu kan sanarwar haɗin gwiwa daga ƙasashe fiye da 20.
Nijeriya ta yi watsi da amincewar da Isra’ila ta yi wa Somaliland a matsayin 'yantacciyar ƙasa
Nijeriya ta bi sahun Tarayyar Afirka da waus kasashen da dama wajen watsi da amincewa da kasar Somaliland da Isra'ila ta yi. / Reuters
3 awanni baya

Nijeriya ta yi watsi da matakin da Isra’ila ta ɗauka na amincewa da Somaliland a matsayin ƙasa mai ‘yancin cin gashin kai, tana mai gargadin cewa matakin ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma yana barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin Kusurwar Afirka.

A ranar Juma'a Isra'ila ta zama ƙasa ta farko da ta amince da Somaliland a hukumance, yankin da ya ayyana kansa a matsayin ƙasar da ta ɓalle daga Somalia a shekarar 1991 bayan yaƙin basasa, amma Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta taɓa amincewa da ita ba.

Nijeriya ta fitar da wata sanarwa ta daban da ke yin Allah wadai da matakin na Isra'ila. Ta kuma sanya hannu kan sanarwar haɗin gwiwa daga ƙasashe sama da 20.

A cikin sanarwar da ta fitar a ƙarshen mako, Nijeriya ta ce "ba tare da wata shakka ba" tana goyon bayan 'yancin kai, haɗin kai da kuma haƙƙin mallakin Somalia.

Masu AlakaTRT Afrika - Eritrea ta nemi Kwamitin Tsaro na MDD ya yi martani kan amincewar da Isra'ila ta yi wa Somaliland

"Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake nanata alƙawarinta na ci gaba da bin ƙa'idojin 'yancin kai, mutuncin yankuna da 'yancin siyasa na dukkan Mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Afirka," in ji Kimiebi Ebienfa, mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya.

Nijeriya ta ƙara da cewa ta amince da gwamnatin Somalia a matsayin "halastacciyar hukuma da ke wakiltar al'ummar Somalia" kuma ta yi Allah wadai da duk wani mataki da ke kawo cikas ga tsarin kundin tsarin mulkin Somalia.

"Gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga ƙasashen duniya da su daina amincewa da wani ɓangare na yankin Somalia a matsayin wata ƙungiya mai zaman kanta, domin irin waɗannan ayyukan za su ƙara ta'azzara rikicin ne kawai," in ji sanarwar.