Akalla mutane 25 ne aka tabbatar sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a Jihar Yobe na Najeriya, in ji jami'ai a ranar Lahadi.
Lamarin ya faru a daren Asabar lokacin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 52 ya kife ya kuma nutse yayin da yake tafiya daga garin Adiyani a Karamar Hukumar Guri ta jihar Jigawa zuwa Garbi a Karamar Hukumar Nguru ta jihar Yobe.
An ceto fasinjoji 13, yayin da rahoton farko na jami'ai ya ce ana ci gaba da neman mutane 14 har yanzu.
Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, Mohammed Goje ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa mutanen sun tafi kamun kifi ne, da noma, da sauran harkokin kasuwanci, lokacin da kwale-kwalen ya kife da su a tsakiyar ruwa.
“ Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe na iya tabbatar da wannan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a cikin kogi a Nguru,” in ji Goje.
“Tawagarmu ta bincike da ceton har yanzu na aiki tare da hukumomin tsaro da 'yan sa-kai na al'umma don nemo waɗanda suka ɓace,” in ji Goje.





















