Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin bunƙasa shirin tallafa wa aƙalla mutum miliyan 10 a Nijeriya ta yadda za su bunƙasa harkar tattalin arzikinsu da rage talauci a ƙasar.
Tinubu ya bayyana haka ne a cikin saƙonsa na sabuwar shekarar 2025 ga ‘yan ƙasar.
“Za mu inganta aiwatar da Shirin Bunƙasa Unguwanni da ke cikin Shirin Farfado da Fata (Renewed Hope), inda muke fatan sanya akalla ‘yan Nijeriya miliyan 10 cikin harkokin tattalin arziki, ta hanyar tallafa wa akalla mutum 1,000 a kowace mazaɓa a duka mazaɓu 8,809 a faɗin ƙasar,” in ji shugaba Tinubu a cikin sakon.
Shugaban na Nijeriya ya kuma bayyana cewa za a habaka tattalin arzikin mutane ta hanyar bunkasa harkokin noma, da cinikayya da sarrafa abinci da hakar ma’adinai.
Tsaro da zaman lafiya
Shugaban Bola Tinubu ya bayyana cewa jami’an tsaro Nijeriya na ci gaba da matsa wa ‘yanta’adda da masu kai hare-hare lamba, musamman a yankin arewacin kasar.
Ya bayyana cewa tun bayan harin da Amurka ta kai a yankin arewa maso yammacin Nijeriya da hadin gwiwar gwamnati, sojoji sun zafafa hare-hare a kan kungiyoyin ta’adda da dabobin miyagu a arewa maso gabas da arewa maso yamma.
Ya ce “A 2026, jami’an tsaronmu da jami’an leken asirinmu za su karfafa hadaka da abokan huldarmu na nahiya da na duniya, don kawar da duk wata barazana ga tsaron kasarmu.”
A cewar shugaban yana da iminin cewa bai wa jihohi damar samar da ‘yansandansu tare da yin aiki yadda ya kamata “abu ne mai muhimmanci wajen magance matsalar ta’addanci, da harkar satar mutane da sauran matsalolin tsaro masu alaka da su.”
Sakon na shugaba Tinubu ya kuma kunshi bayanai kan nasarar da Nijeriya ta samu a 2025 a fannin tattalin arziki da suka hada da raguwar hauhawar farashin kayayyaki da bunkasar ma’aunin tattalin arziki na GDP, da tagomashin kasuwar hannun jari ta Nijeriya inda ta bunƙasa da kaso 48.12 cikin dari.
Sannan ya yi alkawarin cewa, gwamnati ta sha alwashin ci gaba da rage hauhawar farashi a 2026 don amfanin duka ‘yan kasa.





















