Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta kama ma’aikatan jirgin ruwa Indiyawa 22 bayan an gano hodar ibilis, wato cocaine mai nauyin kilogirm 31.5 a cikin jirgin, a gaɓar ruwan Legas.
An yi kamen ne a ranar 2 ga Janairu a wani jirgin ruwa mai suna MV Aruna Hulya “wanda ya taso daga Tsibirin Marshall,” a cewar wata sanarwa da Kakakin na NDLEA Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi.
An jima ana yi wa Nijeriya kallon wata cibiyar samarwa da safarar miyagun kwayoyi da aka nufi kai su Turai da sauran kasashen Afirka.
A watan Nuwamba NDLEA ta ce ta kama ‘yan Philippines su 20 a cikin jirgin ruwa ɗauke da aƙalla kilogiram 20 na cocaine da suka yi safararta daga Brazil sannan suka nufi gaɓar ruwa ta Same.
Tun da farko a cikin watan kuma, hukumar ta ce tana aiki da hukumoin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi na Amurka da Birtaniya wajen bincika wasu gungun mutane da suka shigar da cocaine mai nauyin kilogiram 1,000 da aka gano a cikin wata kwantena a gaɓar ruwan Legas.





















