Fiye da mutane 30 aka kashe, aka sace wasu da dama a wani hari da 'yan fashin' daji suka kai a Jihar Neja ta tsakiyar Najeriya, in ji 'yan sanda a ranar Lahadi.
Maharan sun kutsa kauyen Kasuwan Daji a karamar hukumar Kabe, suka ƙone kasuwa kafin su kwashe kayan shaguna domin neman abinci.
"Fiye da mutane 30 ne suka rasa rayukansu yayin harin, wasu mutanen kuma an sace su," a lokacin fashin ranar Asabar, in ji Wasiu Abiodun, kakakin 'yan sandan Neja.
Gungun masu satar mutane, wadanda mazauna ke kiran su 'yan fashin daji, suna yawan sace jama'a don neman kudin fansa da kuma fashi a ƙauyuka a wasu sassan arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar Najeriya.
Wajen da matsalar ta yi ƙamari
Jihar Niger ta kasance ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fuskantar wannan matsalar a 'yan watannin da suka gabata.
A watan Nuwamba, wasu gungun ‘yan bindiga sun sace fiye da ɗalibai 250 da ma'aikata daga wata makaranta a jihar.
Hukumomi sun sanar da sakin su makonni bayan satar.
Gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙoƙarin inganta tsaro bayan jerin sace-sacen. Yawancin wadanda aka sace kwanan nan an riga an ceto su.





















