Yadda Afirka ta zama nahiya mafi fama da kaɗaici a duniya
AFIRKA
6 minti karatu
Yadda Afirka ta zama nahiya mafi fama da kaɗaici a duniyaWani rahoton WHO ya bayyana cewa a kowacce awa daya kadaici na kashe mutane 100 a duniya inda kuma mu’amala a tsakanin al’umma ke kara lafiya, tsawon rai da amfanin rayuwa, hakan ya zama shaidar cewa mu’amalar dan adam magani ne mai muhimmanci.
Yadda Afirka ta zama nahiya mafi fama da kaɗaici a duniya / Getty Images
10 awanni baya

Littafin E.M. Forster mai suna Howards End na shekarar 1910 ya fara da wani rubutu mai ban sha'awa mai taken "Kawai ka yi hulda". Amma me zai faru idan tushen alaƙar ɗan adam ya fara wargajewa?

A farkon wannan shekarar, tsohon ministan lafiya na Kenya, Dr Cleopa Mailu, ya fuskanci wata gaskiya mai ban daci: kusan kashi ɗaya cikin huɗu (24%) na al'ummar Afirka sun ba da rahoton kasancewa a cikin kaɗaici, inda matasa 'yan shekara 13 zuwa 17 suka fi shan wahalar matsalar.

Bayanan, wani ɓangare na rahoton duniya ne na Hukumar Haɗin Kan Jama'a ta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), kuma ya kusan zama akasin abin da Mailu ya yi tunanin zai gani.

Ya kasance koyaushe yana tunanin kaɗaici wani tsari ne na ƙasashen yamma wanda Afirka, saboda al'adarta ta iyalai masu faɗi da rayuwar al'umma, ba za ta fuskanci matsalarsa ba.

Abin mamaki, sabon rahoton WHO ya nuna cewa idan aka kwatanta da Afirka, kusan kashi 10% ne kawai na mutanen Turai suka fuskanci kaɗaici.

"Na yi zaton duk wannan yana faruwa a Arewacin Duniya, kuma muna zaune lafiya a nan," Mailu ya shaida wa TRT Afrika. "Amma idan ka zurfafa ka fahimci yadda tsarin zamantakewarmu ya lalace a cikin shekaru 70 zuwa 80 da suka gabata, za ka fara fahimtar dalilin hakan."

Samuwar rabuwa da juna

Masana zamantakewa sun yi imanin cewa, cusawa al'umma al’adun yammacin duniya ya canza salon rayuwar Afirka, yana wargaza alaƙar da ta taɓa haɗa al'ummomi.

"Shekaru kaɗan da suka wuce, idan kai yaro ne da kake girma a ƙauye, mahaifiyarka ba ta damu da inda ta bar ka ba. Akwai kaka ko maƙwabci da ke kula da yaron. Mahaifiyar za ta yi ayyukanta ba tare da damuwa game da lafiyar ɗanta ba. A yanzu hakan ba zai yiwu ba kuma," in ji Mailu.

"A yau, idan ka kai 'ya'yanka ƙauye, suna cikin damuwa saboda ba za su iya ma yin magana da kakarsu ba."

WHO ta bayyana kaɗaici a matsayin jin baƙin ciki da ke tasowa lokacin da aka samu gibi tsakanin dangantaka ta zamantakewa da ake so da ta gaske, yayin da keɓewa ta zamantakewa tana nufin rashin alaƙar zamantakewa. Dukkan su na iya wanzuwa daban-daban; mutum zai iya kasancewa kewaye da mutane amma yana jin kaɗaici.

"An dauke ka aiki kuma kana aiki a ɗakin kwamfuta misali. Kuma daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma kana kebe da na'urori. Idan ka koma gida, kai kaɗai ne a cikin gidanka" in ji Mailu.

“Gudun hijira a fannin tattalin arziki yana ƙara ta'azzara matsalar. Mutane suna barin iyalai a garuruwansu na asali don su zauna a biranen da ba su sani ba ko ma a ƙasashen waje, suna ƙara zama a kebe idan ba su san kowa a can ba kuma wataƙila ma ba sa jin yaren yankin.”

"A zamanin yau, har ma maƙwabta ba sa san juna ba," Mailu ya shaida wa TRT Afrika.

Annobar da ke yaduwa a sirrance

Duk da cewa kaɗaici na iya faruwa a kowane zamani, matasa ne suka fi fuskantar matsalar.

"Ko da a cikin duniyar da ke da alaƙa da fasahar zamani, matasa da yawa suna fama da kaɗaici. Yayin da fasaha ke sake tsara rayuwarmu, dole ne mu tabbatar da cewa tana ƙarfafa haɗin kai na ɗan adam, ba ta raunana shi ba," in ji Chido Mpemba, shugaban kwamitin hula da juna na WHO.

Sakamakon lafiya da kaɗaici da keɓewa ke janyo wa na iya zama mai tsanani, yana ƙara hatsarin shanyewar jiki, cututtukan zuciya, ciwon sukari, raguwar karfin fahimta da mutuwa da wuri.

Rahoton ya bayyana cewa mutanen da ke fama da kaɗaici suna da yiwuwar fuskantar baƙin ciki ninki biyu kuma suna iya fuskantar damuwa da tunanin kashe kansu.

WHO ta danganta kaɗaici da kusan mutuwar mutane 100 a kowace awa, wanda adadin ya kai sama da mutane 871,000 a kowace shekara.

Ƙarfin mu’amala da juna, akasin haka, yana ba da fa'idoji na kariya a tsawon rayuwa, rage kumburi, rage hatsarin rashin lafiya mai tsanani, da haɓaka lafiyar kwakwalwa da tsawon rai.

"Idan muka magance raguwar hulɗa da kulla alakar zamantakewa da lafiyar kwakwalwa, zuba jarin da ake buƙata don magance cututtuka da aka saba da su zai yi ƙasa sosai," in ji Mailu.

Shaidun likitanci sun tabbatar da cewa hulɗar zamantakewa tana haifar da kwayoyin halitta masu kyau, wanda ke ba da gudunmawa ga ingantacciyar lafiya da walwala gaba ɗaya.

Muhimman bukatu da ke gogayya

WHO ta yi kira ga gwamnatoci, al'ummomi da daidaikun mutane da su ɗauki alaƙar zamantakewa a matsayin fifiko ga lafiyar jama'a tare da tasirin ci gaba mai ma'ana.

Amma Mailu yana da damuwar cewa shawo kan shugabannin siyasa don su fifita haɗin kai a zamantakewa zai yi wahala lokacin da ake fafutukar biyan buƙatun da suke a bayyane.

"A ƙarshe za ku sha wahala da abin da kuka yi watsi da shi. Kamar mota ce da ba ta zuwa a duba lafiyarta. Wataƙila za ta lalace, sannan za a tilasta muku gyara ta. Kuma wannan shi ne abin da ƙasashe za su fuskanta," in ji shi yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Wasu ƙasashe sun fahimci wannan ƙalubale. Birtaniya, Norway da Japan suna da ministocin jin daɗin al’umma don magance ƙalubalen ta hanyar shirye-shirye masu kyau, suna mayar da hankali kan kaɗaici da keɓewa a zamantakewa.

Sauyin tunani a zamantakewa

 "Zuba jari a hulɗar zamantakewa ba lallai ne ya buƙaci sabbin abubuwa masu yawa ba," in ji Mailu. "Suna buƙatar wayar da kai. Ba na buƙatar wasu manyan abubuwa don haɗuwa da maƙwabcina, amma ina buƙatar canza tunanina don mu iya mu'amala."

WHO ta yi kira ga mutane da al'ummomi da su haɓaka al'adar mu’amala da juna. A tsakanin wasu al'ummomin Asiya, gidaje masu mutane da yawa har yanzu suna da dama, suna ƙarfafa salon rayuwa wanda ke haɓaka alaka da juna a zamantakewa.

"Wasu daga cikin mu sun bar wasu daga cikin waɗannan tsare-tsare, suna tunanin cewa na kauyanci ne ko zamanin baya Amma a nan ne mafita take," in ji Mailu.

A cikin nahiya kamar Afirka, inda gine-ginen gargajiya suka sha wahala da zaizayewa hankali, mayar da hankali kan gina abubuwan more rayuwa kamar dakunan zaman al'umma a manyan rukunin gidaje na zama zai iya taimakawa wajen magance annobar kaɗaicin.

"Muna buƙatar rungumar makoma tare da kayayyakin more rayuwa waɗanda ke taimaka mana mu tsira, mu haɗu kuma mu sami kwanciyar hankali," in ji Mailu ga TRT Afrika.