| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Wane ne Liam Rosenior, sabon kocin Chelsea?
Ranar Litinin 5 ga Janairun 2026 ne Liam Rosenior ya karɓi muƙamin sabon kocin Chelsea, wanda ya maye gurbin Enzo Maresca da aka sallama.
Wane ne Liam Rosenior, sabon kocin Chelsea?
Shekarun Liam Rosenior 41 a duniya. / Reuters
6 Janairu 2026

Liam Rosenior shi ne sabon kocin da ya karɓi ragamar ƙungiyar Chelsea ta Ingila, mako guda bayan da aka sallami Enzo Maresca. Rosenior ɗan asalin Ingila tsatson Sierra Leone, kuma yana da shekaru 41.

Tsohon kocin Strasbourg tsawon watanni 18, Rosenior ya bayyana naɗa shi manajan Chelsea a matsayin wata “girmamawa” da bai yi tababar karɓa ba.

Sabon kocin ya jaddada cewa Chelsea babbar ƙungiya ce da ta lashe kofunan Zakarun Turai, kuma komawarsa Stamford Bridge za ta ba shi damar baro Faransa don komawa wajen iyalansa a Ingila.

Kocin da ake yi wa kallon mai ƙarancin shekaru, yana kallon sabuwar ƙungiyar a matsayin babban cigaba kasancewar zai bar gasar Ligue 1 ta Faransa zuwa gasar Firimiya.

Kafin 2024 sanda ya maye gurbin Patrick Vieira a Strasbourg, Rosenior ɗanwasan baya ne da ya buga wa ƙungiyoyin kamar Hull City, Brighton, Reading, Fulham, da Bristol City.

Wane ne Liam Rosenior

Liam Rosenior ya yi ritaya a 2018, sannan ya fara aikin sharhin labaran wasanni a tashar Sky Sport. Dagan nan ya zama kocin ƙaramin kulob ɗin Brighton na ‘yan ƙasa da shekara-23.

Daga bisani, ya zama mataimakin kocin ƙungiyar Derby ta Ingila, Phillip Cocu. Bayan tafiyar Cocu a 2020, Rosenior ya ci gaba da taimakawa sabon kocin Derby, Wayne Rooney.

Rosenior ya zama babban koci a karon farko a Hull City da ke buka ƙaramar gasar Championship ta Ingila, inda ya kai su matsayi na bakwai a teburi a kakar 2023-24.

A bazarar 2024, Rosenior ya zama kocin Strasbourg mai buga babbar gasar Ligue 1 ta Faransa, wadda kuma ke ƙarƙashin kamfanin BlueCo da ya mallaki Chelsea.

A yanzu dai Rosenior ya karɓi Chelsea tana mataki na 5 a teburin Firimiya da maki 31 daga wasanni 20. Kuma zai gaji muƙamin da a shekarun nan ake yawan korar mutum idan ya gaza.

Chelsea ta yi koci shida a shekaru biyar, waɗanda suka haɗa da Jose Mourinho, Frank Lampard, Thomas Tuchel, Graham Potter, Mauricio Pochettino, da na ƙarshe, Enzo Maresca.