DUNIYA
2 minti karatu
Amazon da Microsoft sun buƙaci ma’aikatansu su zauna a Amurka bayan bizar H-1B ta koma $100,000
Bayan dokar da Trump ya saka wa hannu, duk wani kamfanin Amurka da ke so ya ɗauko ma'aikaci daga ƙasar waje, sai ya rinƙa biya wa ma'aikacin dala 100,000 a duk shekara a matsayin kuɗin biza.
Amazon da Microsoft sun buƙaci ma’aikatansu su zauna a Amurka bayan bizar H-1B ta koma $100,000
Amazon ne kamfanin da ya fi ma’aikata da ke da bizar H-1B a bana, inda ya samu fiye da 10,000, sai kuma Tata Consultancy, Microsoft, Apple da Google. / Reuters
20 Satumba 2025

Kamfanonin Amazon, Microsoft da JPMorgan sun gargadi ma’aikatansu masu takardun izinin zama na H-1B da H-4 da su zauna a Amurka kuma su guji tafiya zuwa ƙasashen waje bayan Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan wata doka mai girma da ke sauya tsarin izinin aiki ga kwararru.

Bayanan cikin gida da imel sun nuna cewa kamfanonin suna ba da shawara ga masu izinin zama da ke ƙasashen waje a halin yanzu su dawo Amurka kafin karfe 12:01 na safe ET a ranar 21 ga Satumba, lokacin da sabbin dokokin za su fara aiki, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Umarnin Trump, wanda ya saka wa hannu a ranar Juma’a a Ofishin Oval, yana bukatar kamfanoni su biya harajin shekara-shekara na $100,000 ga kowanne izinin H-1B, matakin da gwamnatin ke cewa an yi shi ne don kare ma’aikatan Amurka.

Amazon ne kamfanin da ya fi ma’aikata da ke da bizar H-1B a bana, inda ya samu fiye da 10,000, sai kuma Tata Consultancy, Microsoft, Apple da Google.

Shirin H-1B, wanda aka ƙirƙira a shekarar 1990, yana ba kamfanonin Amurka damar ɗaukar kwararrun ma’aikata daga ƙasashen waje a fannonin kimiyya da fasaha, amma ya daɗe yana fuskantar suka kan cewa yana rage albashin ma’aikata.