| Hausa
WASANNI
1 minti karatu
Maroko ta yi nasara kan Comoros da ci 2-0 a farkon Gasar AFCON 2025
Ƙasa mai masaukin baƙi Maroko ta doke Comoros da ci 2-0 a wasansu na farno na gasar AFCON 2025.
Maroko ta yi nasara kan Comoros da ci 2-0 a farkon Gasar AFCON 2025
Maroko ta doke Komoros 2-0 a wasan farko na gasar cin kofin Afirka ta 2025, a ranar 21 ga Disamba, 2025. / Reuters
22 Disamba 2025

Masu masaukin baƙi, Maroko ta doke Comoros da ci 2-0 a wasan buɗe AFCON 2025 da aka buga a filin Prince Moulay Abdellah a babban birnin Rabat ranar Lahadi.

Brahim Diaz ya fara cin ƙwallo ga tawagar mai taken 'Atlas Lions' a minti na 55. Ayoub El Kaabi ya ƙara ta biyu a minti na 74, wanda ya kai Moroko saman teburin Rukuni A.

Sauran ƙungiyoyin a rukunin sun haɗa da Zambia da Mali, waɗanda za su fafata da juna a ranar Litinin.

An buɗe gasar mai ƙasashe 24 da maraicin Lahadi 21 ga Disamban 2025, wadda za ta gudana zuwa 18 ga Janairun 2026.

A cikin jadawalin Rukuni A na gasar, Comoros za ta buga da Zambia a 26 ga Disamba, rana ɗaya da wadda Maroko za ta fafata da Mali.

Wasannin ƙarshe na zagayen rukuni (Zambia da Moroko, da Comoros da Mali) za a buga su a 29 ga Disamba.

Ƙungiyoyi biyu na saman kowanne rukuni za su ci gaba zuwa zagaye na 16, tare da ƙasashe huɗu masu fifikon maki waɗanda suka ƙare a matsayi na uku.