| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Dubban mutane sun tsere daga Al Fasher bayan mayaƙan RSF sun ƙwace iko da yankin da ke Sudan: MDD
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayyana cewa alƙaluman na farko ne kuma za su iya sauyawa a yayin da rashin tsaro ke ci gaba kuma ake ta yawan samun rasa matsugunai.
Dubban mutane sun tsere daga Al Fasher bayan mayaƙan RSF sun ƙwace iko da yankin da ke Sudan: MDD
Mayakan RSH na rike da iko da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur. / AA / Others
22 Disamba 2025

Fararen-hula 'yan ƙasar Sudan aƙalla 107,000 ne suka rasa matsugunansu a birnin Al Fasher da ƙauyukan da ke kewaye da shi a Jihar Darfur ta Arewa sakamakon rashin tsaro da ke ƙara ta'azzara, in ji Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗuniya (IOM).

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, hukumar ta ce kimanin mutum 107,294, daga iyalai 24,221, sun tsere daga Al Fasher da yankunan da ke kusa da shi a tsakanin 26 ga Oktoba zuwa 8 ga Disamba lokacin da mayaƙan RSF suka karɓe iko da birnin, yayin da yanayin tsaro ya taɓarɓare sosai a yankin.

Kimanin kashi 72 cikin ɗari na waɗanda suka rasa matsugunansu sun kasance a cikin yankin Arewacin Darfur, galibi a arewa da yammacin jihar, yayin da kusan kashi 19 cikin ɗari kuma suka yi ƙaura zuwa wasu jihohi, ciki har da Tsakiyar Darfur, Jihar Arewa da Jihar White Nile, in ji IOM.

A cewar tawagar da ke aiki tare da jama’a ta hukumar, kusan kashi 75 cikin ɗari na waɗanda suka rasa matsugunansu tun daga 26 ga Oktoba sun riga sun rasa matsugunansu ne a cikin gida, daga ciki har da mutanen da suka fara tserewa daga manyan sansanonin 'yan gudun hijira, kamar Zamzam da Abu Shouk, ko unguwannin da ke cikin Al Fasher a lokacin da aka fara samun ƙaruwar tashin hankali.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa takunkumin zirga-zirga da rashin tsaro mai ɗorewa na iya ƙara taƙaita kai komon jama’a da kuma canza hanyoyin ƙaura dangane da abubuwan da ke faruwa a ƙasa.

Alƙaluman na farko ne kuma za su iya sauyawa a yayin da rashin tsaro ke ci gaba kuma ake ta yawan samun rasa matsugunai, in ji IOM, inda ta ƙara da cewa lamarin yana ci gaba da taɓarɓarewa da ƙaruwar tashin hankali.

An shafe makonni aka ba-ta-kashi tsakanin sojoji da mayaƙan RSF a jihohin Kordofan uku, Arewa, Yamma, da Kudu, wanda ya tilasta wa dubban mutane barin matsugunansu.

Daga cikin jihohi 18 na Sudan, mayaƙan RSF na da iko da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur a yamma, amma sai dai wasu yankunan Arewacin Darfur na ƙarƙashin ikon sojojin Sudan.

Haka su ma sojojin, suna riƙe da iko da mafi yawan yankunan sauran jihohi 13 a kudu, arewa, gabas, da tsakiyar ƙasar, ciki har da babban birnin Khartoum.

Rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da RSF, wanda aka fara a watan Afrilun 2023, ya kashe dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyin wasu tserewa.