Lokacin da Halima Cissé 'yar kasar Mali ta haifi jarirai tara a watan Mayun 2021, labarinta ya bazu a intanet.
Matar da likitoci suka yi zaton tana tsammanin jarirai 7, sai kawai ta haifi 'ya'ya mata biyar da maza huɗu da suka tsira a tarihin duniya - 'yan mata biyar da maza huɗu da aka haifa bakwaini a mako na 30.
A yankinta na asali na Afirka, inda ake ɗaukar iyali mai yawa a matsayin albarka, labarin ya tayar da hankali fiye da kawai jin tsoro mai ban mamaki.
Halima da jariranta ba wai kawai abin mamaki ne na likitanci ba, sun zama alamar matsawa daga gasjkiyar al’amari na zamani ko ma boyayye da ya shafi miliyoyin ma’aurata: rashin haihuwa.
"Akwai ra'ayin cewa Afirka ba ta da matsalolin haihuwa," in ji Dr. Wanjiru Ndegwa, mai bayar da shawara kuma ƙwararriyar likitar haihuwa a Cibiyar Kula da Haihuwa ta ‘Footsteps To Fertility Centre’ da ke Nairobi a Kenya, yayin tattaunawa da TRT Afrika.
"Kwanan nan na halarci wani taron karawa juna sani kuma wani farfesa daga Jamus ya bayar da shawarar cewa bai kamata a ɓatar da kuɗaɗen da ake kashewa kan matsalolin haihuwa a Afirka ba saboda nahiyar ta riga ta cika da mutane. Ka yi tunanin mamakin da na ji yayin da na ji irin wannan magana."
Yawan jama'a ba shi da alaƙa da matakan haihuwa a kowane yanki. Ƙasa na iya samun miliyoyin mutane kuma har yanzu tana fuskantar matsalolin rashin haihuwa da yawa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana rashin haihuwa a matsayin rashin iyawar ma'aurata su yi ciki bayan watanni 12 ko fiye na ƙoƙari.
Duba ga bayanai na duniya, matsalar na shafar mutum ɗaya cikin shida da ke da shekarun haihuwa a wani lokaci na rayuwarsu.
"Rashin haihuwa na ɗaya daga cikin ƙalubalen lafiyar jama'a da aka fi watsi da su a zamaninmu kuma babban batu ne na rashin daidaito a duk duniya," in ji babban daraktan WHO Tedros Ghebreyesus.
"Miliyoyin mutane suna fuskantar matsalar su kadai. Suna keɓe kawaunansu saboda tsadar neman magani, ana tura su zuwa ga magunguna masu araha waɗanda ke da hatsari kuma ba a tabbatar da su ba ko kuma ana tilasta musu su zaɓi tsakanin fatansu na samun yara da tsare kuɗinsu."
Ka’idoji na farko na duniya
Ka’odojin farko na WHO na ƙasa da ƙasa kan rashin haihuwa, wanda aka fitar a watan Nuwamba, na da nufin inganta rigakafi, gano matsalar da maganinta.
Shawarwari 40 da aka ambata na da inganci a kowane mataki yayin da sake bayar da shawarar haɗa kula da lafiyar haihuwa cikin dabarun kiwon lafiya na ƙasa, ayyuka da kuɗaɗen tallafi.
"A zahiri muna rasa komai ne. Ba mu da isassun ƙwararru waɗanda suka fahimci yadda ake sarrafa rashin haihuwa. Ba mu da isassun cibiyoyin IVF.
“Ba mu da likitocin kula da karamin tayi da ke ciki. Ba mu da cibiyoyin da ke bayar da irin wannan horo," in ji Dr Wanjiru.
Shawarwari da ka’idojin na WHO sun haɗa da shawarwari don samun ingantaccen kula da rashin haihuwa a asibiti.
Suna kuma kira da a ƙara saka hannun jari a rigakafi, gami da bayanai kan haihuwa da rashin haihuwa, abubuwan da suka shafi shekaru, ayyukan da ake yi a makaranta, kula da lafiya a matakin farko da cibiyoyin kiwon lafiyar haihuwa.
Matsin lambar nuna kyama
Matsin lambar zamantakewa ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke tattare da rashin haihuwa, musamman ga ma'aurata da ake tsammanin suna da lafiya.
A tsakanin al'ummomin da suka rike al'ada, galibi ana zargin mata da rashin iya ɗaukar ciki bayan aure, wanda hakan ke haifar da ƙyama wanda galibi ya samo asali daga jahilci.
"Idan ana maganar rashin haihuwa, ba ma'auratan kaɗai ba ne abin ya shafa. Al'umma tana shiga tsakani, tana haifar da ƙyama da ke da alaƙa da hakan," Dr Wanjiru ta shaida wa TRT Afrika.
"Har zuwa yau, ko kafin ta yi aure, mace tana fuskantar matsin lamba don ta bi ra'ayin cewa dole ne ta samu iyali ta hanyar haihuwa. Al'umma tana cewa, 'Muna godiya da digirinku amma kuna da wani muhimmin aiki da za ku cika'."
Saboda haka, shin tambayoyin da suka shafi rashin haihuwa suna kan mata ne kawai?
Dr Wanjiru ta nuna cewa asibitoci a Kenya suna shaida ƙaruwar maza da ke neman shawara ko magani, wanda ke nuna cewa ƙarin abokan hulɗa maza yanzu sun yarda cewa matsalar na iya kasancewa tare da su ko kuma suna buƙatar zama ɓangare na mafitar da ake nema.
Magungunan da ake da su
Ka’idojin WHO suna jaddada buƙatar magance matsalolin da ke haifar da rashin haihuwa, ciki har da cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i ba tare da magani ba da kuma shan taba.
Ana ba da shawarar samar da canje-canje a salon rayuwa - cin abinci mai kyau, motsa jiki da daina shan taba - ga mutane da ma'aurata da ke shirin ko ƙoƙarin samun ciki.
Likitoci sun ce ilmantar da mutane da wuri game da haihuwa da rashin haihuwa zai iya taimaka musu su yanke shawara kan tsarin iyali mai kyau.
Amma yaushe ya kamata mutum ya yi bincike ko ya nemi maganin haihuwa?
"Na ga ma'aurata waɗanda suka kasance tare tsawon wata ɗaya kuma ina mamakin cewa ba su yi ciki ba. Ina gaya musu ba lallai ba ne hakan ya faru cikin wata ɗaya.
“Ina ba su shawara su gwada ɗaukar ciki na akalla shekara guda kafin mu damu. Ba na tsammanin akwai buƙatar yin gaggawar yin gwaji da wuri ko akai-akai," in ji Dr Wanjiru.
Da yake bayyana cewa rashin haihuwa na iya haifar da baƙin ciki, damuwa da kaɗaici a cikin al'umma, ka’idojin WHO sun jaddada buƙatar tabbatar da ci gaba da samun tallafin zamantakewa ga duk waɗanda abin ya shafa.
WHO ta kuma yi kira ga ƙasashe da su sake duba manufofin kiwon lafiya na cikin gida da kuma sa ido kan yanayin rashin haihuwa.
Samun nasarar aiwatar da dabarun yaƙi da wannan matsala mai taso wa na buƙatar haɗin gwiwa a tsakanin ma'aikatun kiwon lafiya, ƙungiyoyin ƙwararru kula da lafiya, ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin marasa lafiya.
Masana sun ce akwai magunguna, amma sun dogara ne kawai akan takamaiman dalilan da ke sa mutum ko ma'aurata ba za su iya ɗaukar ciki ba.
"Akwai mafita. Maganin da ya dace ya dogara ne akan abin da ke haifar da rashin haihuwar," in ji Dr Wanjiru ga TRT Afrika.
Ga yawancin ma'auratan Afirka da ke fuskantar rashin haihuwa, ƙalubalen yanzu shi ne a rage gibin da ke tsakanin sanin cewa akwai magunguna da kuma zaɓar wadanda suka dace.

















