Jami'ai sun ce wani gangamin bayar da gudunmawa da nufin sake gina lardin Aleppo da ya lalace a Syria ya tara dala miliyan 150 a ranar Alhamis, wanda hakan ke nuna babban ci gaba a fannin kudi ga kokarin sake gina daya daga cikin yankunan da suka fi fama da matsala a kasar.
An kaddamar da gangamin na kwanaki uku a karkashin jagorancin Fadar Gwamnan Aleppo, wanda ke neman samar da kudaden da za a mayar da kayayyakin more rayuwa, gidaje, da ayyukan jama'a bayan fiye da shekaru goma na yaki da ya barke a birnin.
Mashirya taron sun ce za a yi amfani da kudaden ne ga ayyukan ci gaba da ake bukata cikin gaggawa don farfado da rayuwar yau da kullum a cibiyar kasuwanci ta tarihi.
Aleppo ya fuskanci wasu daga cikin rikice-rikice mafi zafi a lokacin yakin basasar Syria, inda unguwannin garin suka lalace kuma muhimman ayyuka cibiyoyin ayyuka suka gurgunce.
Duk da kawo karshen fadace-fadace, birnin na ci gaba da fuskantar kalubalen sake gina shi, wanda ya haifar da irin wannan yunkurin na tara kudi a wasu larduna.
Cigaba da kai hare-hare daga Isra’ila
Wannan gangamin ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke kara kai hare-hare Syria, wanda Damascus ta ce ya kara kawo cikas ga murmurewar kasar.
Bayanan gwamnatin Syria sun nuna cewa tun daga Disamban 2024, Isra'ila ta kai hare-hare ta sama sama da 1,000 a fadin kasar da kuma hare-hare sama da 400 a kan iyakokinta zuwa lardunan kudu, inda ta kashe fararen hula da kuma lalata cibiyoyin soji da kayayyakin more rayuwa.
Bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad a karshen shekarar 2024, Isra'ila ta kuma fadada mamayar da take yi a Tuddan Golan na Syria ta hanyar kwace wani yanki mai tsaro da ba shi da makami - matakin da Syria ta ce ya saba wa yarjejeniyar janyewa daga yankin ta shekarar 1974.
Jami'ai sun ce ci gaba da tallafa wa kasashen duniya da na cikin gida zai zama muhimmi idan Aleppo za ta sake ginuwa bayan shekaru na yaki da kuma tashin hankali a yankin.

















